HALIN YAU 25 & 26

🌺 *HALIN YAU*!🌺




·•·•·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·•·•·•
*_LAFAZI WRITERS ASSOCIATION ®_* ✍️
───────────────────────
```{Kyakkyawan lafazi a cikin rubutu yana ɗamfare da bin ƙa'idar Adabin Hausa.```

```Lafazi gidan karamci da mutuntaka, Harshenmu abin alfaharinmu.}``` ✏️✏️✏️
____________(✪)______________

https://mobile.facebook.com/Lafazi-Writers-Association-104448621878916/
•·•·•·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·•·•·•



 *SADAUKARWA GA*
 *SADIK ABUBAKAR*.



               25_26.





Kwanci tashi har jarrabawar mock ta fito cikin ikon Allah Sa'adatu ba ta sami matsalar komai ba tasan kuma MK ya taka muhimmiyar rawa ga samun nasararta, tunda a sanadin matsin da yake mata yasa ta zama cikin jerin daliban da suke nacin karatu. 

A wannan term din kuma ta tsinci kanta da jin haushi idan ta gan shi da Farida, gashi dai ta tsane shi, amma ko yaya ta gan shi da ita, musamman da ya kasance Farida Prepect ce, kuma mafi yawa idan shi ne Duty Master, to kuwa za ta kasance Duty Prefect, sai ta ji ranta ya mugun 'baci.

A yanzu tafi jin takaicin 'kokarin da Farida take da shi fiye da komai cikin FGC.

Kasancewar Farida na cikin daliban da suke wakiltar makarantar gaba'daya, dan yanzu ma shirin tafiya Lagos gasar Cowbell Competition suke yi, tunda sun cinye na jahar Kano, yanzu matakin 'kasa zasu tafi, kuma Uncle MK din na cikin tawagar Malaman da za suyi masu rakiya zuwa birnin na Ikko.

Wannan dalilin sai ta sake zama so mute, ita kadai ta san mai ta ke going through a zuciyarta.

Kullum idan ta zauna ta dinga bincikar kanta, me yasa ilimin Monica Paul bai dame ta ba?me yasa Khalil Ibrahim da yake da 'kokarin shima bai dameta ba, tunda har da shi za'ayi ma tafiyar?
Kanta har zafi yake dauka akan wannan tunanin.
Kyashi take mata ko kuwa hassada ne?.

Kullum kuma indai ta ga Farida, a ranta sai tace, oh ance mutum tara yake bai cika goma ba, komi da ake so Farida ta hadasu, doguwar mace, Fara tas, mai dogon gashi, mai ha'kuri, mai tarin ilimi gashi ta yi sa'ar fitowa a gidan wadata, kawai dai ba ta da dirin jiki, sai tsananin kyaun fuska.
siririyace ta sosai, shiyasa komi na jikinta 'karami ne.
Sannan kuma ta lura bata da cikakkiyar lafiya wadda takan shafe sati idan ciwon ya tashi ba tazo ba. wannan ciwon da rashin cika irin ta cikkakun mata, shine tawayar da tasa bata cike goma cif cif ba.

Tauraron Farida ya sake haskawa ne bayan sun yi nasarar zuwa na 'daya a gasar da suka yi, wadda itace tafi bada amsa a tsakanin Monica da Khalil.

Kowa nan nan yake da ita tunda ga kan principal da sauran teachers, dama student gaba daya.
Wannan ya sake sa tsanar ta a zuciyar 4stars da suke jin su din isassu ne.

A kuma wannan term din Sa'a ta dage, ta 'kure malejin jarumta, ta dau ki 8th position, wadda shine sakamakon farko mafi kyau a tarihin rayuwarta, dan ko a makarantar da ta baro, double lamba take dauka, bare wannan makarantar da ta ha'da za'kwa'kuran 'dalibai.

Wannan sakamakon shine mafarin dai na 'yar tsamar su da Uncle Mukhtar, duk 'karshen zangon karatu ya wajabta wa kanshi bawa daliban ajin nasa daga na daya zuwa na uku kyautar 'karfafa guiwa, a matsayin sa na class master dinsu, a A class ya bawa Farida.
A wannan karon har Sa'adatu ya bawa kyautar the most hardworking student in the class, Kamar kullum Khalil Ibrahim ke daukan 1st position, shi ya 'Kira a 'karshe bayan ya bawa Sa'a. da monicca as 2nd, da wani Abdulrashid da ya zo na uku.amma da yaje karba sai yasa left hand ya Kuma juya fuskar shi, wannan rashin 'da'a da ya nuna ya hassala Mk ya fasa bashi kyautar ya kuma hukunta shi ta hanyar sa shi, sharar school area.

Tunda ga nan aka fara cece kucen son Gogel yake banda haka, ta yaya ga Halima ta zo ta hudu bai bata ba, ga na biyar, duk ya tsallake ya tafi Kan 8? asalima sai da wannan kyautar ya kawo mata matsala tsakanin ta da Khalil da kuma Halima.

Na Halima kyashi ne, shikuma Khalil kishi ne, gani ya ke kawai soyayya suke yi amma ai kowa yasan yadda ya takura mata, menene dalilin gift din? alhalin akwai wadda suka fita cancanta amma bai basu ba.

Kusan wannan ta'kardamar ne dalilin afkuwar soyayyar ta su dan ta dade tana jin kishinsa akan Farida bata gane kishi bane sai a wannan lokacin daya sake da ita, ya gamsu tana karatu kamar yadda ya kamata.

Ranar juma'ar da akayi hutu, tana cikin ranakun da bata Mantawa cikin rayuwar ta a makaranta, a ranar ne ta nutsu ta 'kare mishi kallo na tsanaki, a lokacin da ya shigo dan ya musu bankwana sai kuma bayan hutu.

Dogon saurayi mai matsakaicin jiki, ma'ana siriri ne, amma kuma bashi da rama ko kadan kai tsaye za'ace mishi fari, duk da idan irin su Farida na gun, duhunsa za'a gani, doguwar fuska mai dauke da dogon hanci, da madaidaitan idanuwa, farare tas, da zagayayyen 'karamin baki mai dauke da 'kananun ha'kora jerraru, ya kuma zagaye bakin da gemu. yanayin sa tamkar 'kani ne ga tauraron wasan kwaikwaiyon nan Yakubu muhd saboda yadda suke yanayi.

sanye yake cikin shadda fara 'kal, ma'abocin tara suma, mai kuma yawan gyarata dan kullum comb din shi na aljihunsa, hular yan bautar 'kasa ya saka, kafar sa dauke da open takalmi ba'ki, hannunsa daure da agogon silver samfurin (D&G). tun kuma a lokacin yake amfani da turaren Versace,'kamshin sa na cikin abubuwan da dalibai ke magana akai. 

A wannan kallon da ta mishi na 'kurillah ta janyo wa kanta, domin bata dauke idon ta akan shi ba, sai da son shi ya cika zuciyar ta dam, irin son nan da yake shiga ba tare da an ankaraba, lokacin da za'a ankare din ya riga da yayi illar da ba yadda za'ayi dashi.

Da kanta ta dinga cewa Madallah da 'ka'idojin musulunci, sai da akace kallon shari'a 'daya ne tak, amma ni na mishi kallon 'kwal uwar 'daka.


 Nasiha ya musu, akan ko a gida su dinga bitar karatunsu, su kuma zama yara masu tarbiya, ta yadda duk inda aka ga 'dalibin FGC KANO aga ya banbanta da na kowacce makaranta soboda ladabi.

'karshe ya kulle bayanin shi da lallai su kyautata wa iyayen su, su musu biyayya, su kuma taimake su akan sha'anin ayyukan gida.

Ya kalli side din maza yace 
"wadda kuke tu'ki, ku bi a hankali kusa nutsuwa".

Banda kallon shi ba abin da Sa'a keyi tana jin turancin sa tamkar Baturen da yanke wa yaren cibiya.

Yana kammala wa yayi waving hannun shi alamar bye, ya fice da sauri.

Basu bar class din ba sai da Safina ta yi sulhu a tsakanin Halima matazu da Sa'adatu Gogel, dan haka rabuwa suka yi ta salin alin a tsakanin su tare da al'kawarin zasu hadu a gidan su Humaira asabar din sama, bata gobe ba.

Tafe suke ita da Zainab da Asiya wadda yayar Zainab din ce.
kamar ance ta juya ta hango Uncle Mk da Farida a tsaye jikin wata bishiya da dukkan alamu ba a zo 'daukar ta ba, hira suke hankali kwance.

Take ta ji tamkar ta mutu, zuciyarta ta daure,'kirjin ta yayi nauyi ainun, tafiya kawai take amma bata sanin inda take jefa 'kafarta.
Suna tsaye a bakin gate din makarantar suna jiran abin hawa ta ga yazo ya wuce su akan mashin 'dinsa da a wancan lokacin ake mishi la'kabi da tsuntsun soyayya.
Hannu ya daga musu amma sai ta juyar da fuskar ta, tayi kamar bata ganshi ba, Zainab ce kawai tayi waving 'din shi.

Tana isa gida 'dakin ta, ta wuce ta fa'da kan katifarta wani kuka ya kwace mata, tayi abinta ta 'koshi kasan cewar Innar ta na wanka, daga kukan barci yayi gaba da ita, sanin da mahaifiyar ta yi na fashin salla take yasa bata tashe ta ba.

Haka ta yi hutun nan su ku ku, ciwon so na wahalar da ita, a tunaninta tasan so akan khalil, Ashe ba son sa take ba, kawai shakuwa ne da kuma yadda yake mata hidima, a yanzu ne take dandana azabar soyayya, yanzu ne take jin so tun daga zuciyarta, idanuwanta, da gangar jikinta gaba'daya.

Idan ta tuna Farida yake so, sai taji tamkar za ta sume.
A yadda ta ji ciwon ganinsa da Farida a tsaye yana mata magana cikin walwala komi yana iya faruwa da ita idan ya kasance kullum zata na ganinsa tare da ita.

Zaune ta ke tana fargaban komawar ta makaranta wani satin, a da ta dauka zullimin zuwa makaranta ya 'kare tunda yanzu ta tsira daga tozarcin Uncle Mk! ashe tsugunne bata 'kare mata ba?.

Agogon bango ta kalla taga 2:30pm da sauri ta 'mike ta shiga wanka ta fito ta shirya cikin lallausar atamfar quali-wax mai kalar samaniya(Skye blue)da ratsin ja, Riga da skirt ne, dinkin yayi matuqar zama a jikinta,'katon jan 'dan kunne mai round tasa, a lokacin yayin kwalliya irin ta wannan zamanin ba tazo ba, amma duk da hakan ta she'kawa fuskar ta kwallliyar da ta dace da ita.
Mayafi jah ta ya fa, sumfurin(internet). ta sanya takalmi half-cover amma hills. da yar mitsitsiyar jakarsa wadda zuwanta jos ta siyo su masu Jan duhu. ta fesa turare ta fita zuwa 'dakin Inna.

Inna na shirya, mi'ke wa tayi daga kishingidar da ta yi, hannun ta ri'ke da carbi tunda ta idar da sallar azahar bata tashi ba.

"Yanzu Iyah ba za ki daina zabga turaren nan idan zaki fita ba?
Ba kyau fa, ki kiyayi taba shari'a wallahi"

A hankali tace 
"Allah Inna 'dan ka'dan ne, kawai 'kamshi ne dashi".
"To tunda kin san yadda yake dole ne, idan zaki fita sai kin saka?
Ki fa dinga jin tsoron ubangijin ki, kina kiyaaye ka'idojin shari'a".

Kafin tayi magana, ta sake cewa
"A gabana kika ce da Baffan ku, bayan la'asar za ku dawo, ki sani idan kika wuce wannan lokacin ba zan 'ki fada mishi ba"

"In sha Allah bazan kai maghrib ba Innah"

"Sannan kuma kiji tsoron Allah idan mu bama kallon ki, shi yana kallon ki.
inda kika tambaya nan kawai aka lamince miki zuwa.
Sai kin martaba kanki, kafin wani ya martaba ki, sannan kuma
duk saurayin da ya tsayar da ke kice mishi yazo gidan ku, ya nemi izinin magana dake a wurin mahaifin ki."

A sanyaya ta amsa da
"Zan kiyaye Inna"

Sannan ta juya ta tafi, tana rayawa ko sai yaushe Inna za ta dena mata bitar wannan nasihar a duk sadda zata fita?
Jikin ta yayi sanyi, nasihar ta matu'kar ratsata.
take ta ji ta fasa zuwa inda ta yi niyya, tunda gidan su Halima zata je su hadu da Khalil dake duk kusan unguwar su daya.

Tunda akayi hutu basu hadu ba, a dalilin fushin da yake yi da ita, yana zargin soyayya suke ita da Uncle Mukhtar.

Baisan gidan su ba, kullum cewa take ba a barinta yin zance, sannan indai aka ganshi yaje gun ta za ta Sami matsala babba, nan kuwa gani ta ke da kunya yazo ya ga gidansu.
Nasihar Inna tasa ta canja shawara gara kawai yau ta kaiwa Zainab Ma'aji ziyara ta huta da gorin da ta ke mata na ba ta zuwa gidansu, tunda dama nan ta cewa iyayen ta za ta.

Tana fita yar tafiya tayi 'kadan, tana jiran ta tsallaka, kamar ance 'daga kanki kawai sai idanuwan ta ya fada cikin na shi yana fitowa daga wani shagon aski da ke gaban gidansu kadan.

Mamaki ne ya kamashi ya tsallako ya same ta, tuna nasihar da ya musu na nuna ladabi yasa ta risina tare da fadin

"Barka da rana"
Maimakon ya amsa da hausa sai ya juya harshe, yace

"Sa'adah how are you"? how ur parents and everything?"
A hankali tace"very fine"
Ya sake fadin "are you living here?"
 Kai kawai ta 'daga tare da nuna mishi gidansu "this is our house"
bata san mai yasa shi bata ji, kunyar nuna masa gidan nasu ba, kamar yadda ta ke jin kunyar su Halima da Khalil su ga gidan. duk kuwa da bashi da makusa tunda ginin bulon siminti ne, a shafe yake da filasta, 'kyauren 'kofar shiga lafiyeyye ne mai aminci, sabanin gidajen su 'kawayen nata manyan gates ne dasu, masu zubin mahadi ka ture mussaman gidan su Safina da Humaira Suraj, nasu Halima ne dai ba wani shararren gida bane amma darajar unguwar ma kadai ta kerewa tasu unguwar.

Yayi murmushi tare da fadin "wonderful I know ur father since"

Da mamaki ta kalle shi tace 'Realy"?

"Sosai kuwa for over 5 years, is he around?"

"No yaje Gogel 'dazu"

"Said it in English"

Ta tura baki alamun ya fara son 'kureta wadda shikuma hakan da tayi drives him crazy.
Tace, "He went to our Home town" ta tsuke bakinta ta yi shiru in ma bata yi dai dai ba 'karshen dagewar ta kenan.
 
Murmushi yayi ya sake cewa "oh rude Sa'adah!"
Har cikin ranta take jin dadin yadda ya yanke sunan yake fadin Sa'adah!
Bashine farkon fa'da mata hakan ba, amma shine farkon wadda ya iya fadin sunan, shinea farkon wadda yasa mata son sunan.
Ba zato ta ji yace "where's is ur loverboy"?
Kunyar duniya ta kamata ta yi 'kasa da kai tana jin kamar 'kasa ta tsage ta shige,
Ganin yadda ya kunyata ta, yasa shi tambayar inda zata,
Kai tsaye tace
"Gidan su Zainab Ma'aji".

Sai ya mata sallama, ya tsallaka ya hau mashin dinsa.
ganin haka yasa ta wuce ta nufi gidan su Zainab.

Cike da shauki ta isa gidan su Zainab din, a dakin dake mallakin tane da yayarta Asiya suka zauna, suna hira, tare da Anty Asiya gaba'daya, cike da farinciki take basu labarin haduwarsu da Uncle Mk yanzun nan.
Asiya ta ri'ke baki tana kallon yadda Sa'adatu ke bada labarin shi cike da 'doki da farin ciki, kasa 'boye mamakinta ta tayi, tace
"Sa'adatu da wuri haka?"
Cike da rashin fahimta tace 
Kamar "Yaya da wuri haka, ban fahimce ki ba?"
Cike da iya shege Asiya tace "Ato na ga a duniya kin washi ayi maganar bawan Allah nan, abin mamakin kuma sai gashi yau da kanki kina hirar shi cike da shauki da jin dadi, shine nace da wuri haka har 'kiyayyar ta 'kare?"
Kunya ta kamata sai cewa tayi "Ni fa ba gun ki nazo ba, kuma bada ke nake zance na ba".

Dariya suka sa mata daga Zainab har yayar tata, take kuwa takaicin su ya kamata sai kawai ta fashe musu da kuka.

Nan da nan kuma jikin su yayi sanyi, suka gintse dariyar, suka hau bata ha'kuri, barin ma Asiya da ta ke ta fadin "daga wasa, nifa tsokanar ki nake, to yi ha'kuri ba zan sake ba" 
da ga haka ta mi'ke ta bar musu dakin cike da mamakin shagwaba irin ta Sa'adah.

Da 'kyar Zainab ta shawo kanta ta huce, ta shiga bata labarin tunda akayi hutu basu hadu da Khalil ba, saboda yana fushi da ita akan Mk.
Tabe baki Zainab ta yi tana fadin jimin yaro da 'karfin hali, to shi da nufin sa baza ki kula wani ba? bama shi da hankali.
Sanin da Sa'a ta yi Zainab ba ta yin Khalil, ya sata tsuke bakin ta, har sai da ta gama caccakar shi ta 'kosa dan kanta, ta bar maganar.

Wai a Ina kika ga Uncle Mk din? Zainab ta tambaya cike da son jin 'karshen maganar da Asiya ta so watsawa.
Bata rai ta yi tace inace dariya ku ke min?"
"Ni ba ke na yiwa dariya ba, Yaya Asiya ce ta bani dariya da ta shiga zancen da ba na ta ba".

Numfasawa ta yi tace
 "A 'kofar gidan mu ya fito a wannan shagon na The Boss barbing shop".

Amma dai kin gaishe shi, Zainab ta tambaya da sauri.

"Ah sosai ma har hira mun yi"

Murmushi Zainab tayi tare da fadin
 "In sha Allah wannan ne mafarin hirar taku, ba 'karshe ba"

Da sauri Sa'adah ta dube ta, tace
 "saboda me kika ce haka?"

Kai tsaye ta bata amsa da cewa "saboda kuna son junan ku"
Sunkuyar da kai Sa'adah ta yi tana mamakin yadda ta hasko tana son Mk, sanin Zainab akwai ta da sa ido sai ba tayi mamakin gano ta da ta yi ba.

Kamar zata yi shiru sai ta kasa tace
"Zainab shi ba ya sona, Farida ya ke so", ta fada cikin muryar kuka.

Hannunta Zainab ta ru'ko cikin lallashi tace
"Wallahi yana son ki, ke duk wannan takurar daya miki a banza ce? kin ta'ba tunanin mai yasa ke kadai ya damu ki maida hankali a kan karatun ki?
Ni na dade da gane yana sonki amma irin mutanan ne masu kiyaye doka da oda. kinga ai bai dace ya nuna miki soyayya alhalin aikata hakan laifi ne babba da hukumar makaranta ba za ta amince da shi ba,
Sannan Farida 'daliba ce mai haza'ka irin su farin jini ne da su a gun dukkan malami ba wai Uncle Mk ba kawai. gaskiya ba sonta ya ke, so irin na soyayyar saurayi da budurwa ba, illa 'kaunar da malami yake yiwa dalibarsa mai ladabi da haza'ka".

Cike da gamsuwa Sa'adah ta sake cewa
"Ba kya ganin 'kaunar da ya ke mata zai iya juyewa zuwa irin son dana ke jin tsoro?"
Shiru ta yi na 'dan lokaci,sannan ta nisa tace
"Sa'adah gaskiya zai iya juyewa amma idan kin cigaba da bada 'kofar faruwar hakan".




 
 *Alkalamin Surayya Dee*
               ✍🏼✍🏼
Post a Comment (0)