🌺 *HALIN YAU*! 🌺
·•·•·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·•·•·•
*_LAFAZI WRITERS ASSOCIATION ®_* ✍️
───────────────────────
```{Kyakkyawan lafazi a cikin rubutu yana ɗamfare da bin ƙa'idar Adabin Hausa.```
```Lafazi gidan karamci da mutuntaka, Harshenmu abin alfaharinmu.}``` ✏️✏️✏️
____________(✪)______________
https://mobile.facebook.com/Lafazi-Writers-Association-104448621878916/
•·•·•·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·•·•
*SADAUKARWA GA* *SADIK ABUBAKAR*.
*Gaisuwar fatan alheri ga Zauren Fadila lamido!*
*BA LABARI FANS 2*
_MK DA SA'ADAH NA GAISUWA_🥰.
27_28.
Cike da fargaba ta zuba wa Zainab ido, zuciyarta na bugawa ta ce, "Ban gane ba?"
Muskutawa Zainab din ta yi sannan ta ce "Ina nufin ki toshe dukkan 'kofofin da kika bude na rashin 'da'a a gabanshi, kinga
yanzu ya gamsu kin canja, kin shiga sahun 'dalibai masu dagewa, to ki tattaro dukkan ladabi da nutsuwa ki sanya su a fuskarki da dukkan ayyukanki, ba iya haka ba har a zuciya, ina tabbatar miki idan kika yi haka kin rufe 'kofar da zai dinga miki ganin mai 'karancin tarbiya. Sannan ki yi addu'a, ki bar wa Allah za'bi, idan alheri ne kuma an 'kaddara mijin ki ne, kina zaune Allah zai turo miki shi".
Shiru ta yi tana nazarin maganganun Zainab, wanda ta tabbatar iyakar gaskiya ta fa'da mata.
Ta nisa sannan ta 'dago ta ri'ke hannun Zainab ta ce
Na fahimce ki, na kuma gode da shawarar ki, amma don Allah ki ri'ke mini sirrina."
Murmushi Zainab ta yi tare da cewa, "Ki sa a ranki amana mu
ka yi wannan maganganun, kuma mutum amintacce ne mai 'rike amana. Ina tabbatar miki da ikon Allah baki da matsala da ni"
Haka suka ci gaba da hirarsu, bayan sun yi sallar La'asar ba da jimawa ba, ta musu sallama ta tafi, Zainab ta raka ta har kusan gidansu.
Tunda suka koma makaranta gaba'daya ta mayar da hankali kan karatu, sannan ta bi shawarar Zainab, don haka gaisuwar girmamawa tare da mutuntawa take wa Uncle MK, har ya ji cewa lallai wannan ita ce Sa'adah 'diyar Malam Basiru, waccan da ta gabata ta aro ce. don haka ya daina duk wani gallazawa da yake mata, sai ma wani shiri da yake da ita.
Wanda hakan ya janyo hankalin 'dalibai aka fara gaskata ra'de radin da ake yi cewar son ta yake yi. Wani abin mamakin kuma ita ma Farida sai ta fara jin haushin Sa'adah, tana ganin ta tamkar wata 'yar fashi a soyayya ko mai barazana a rayuwarta. ta san duk yadda take da 'kyaun da ya kai ya kawo, ba ta yaudari kanta ba, ta tabbatar ba za ta nuna wa Sa'adah komai ba, sai fari da gashi da kuma tsayi. Amma batun cikar halitta da kuma boyeyyen kyau da sai an nutsu ake gane shi ta sani Sa'a ta kere mata.
Wata rana sun hadu a Biology Lab, kawai Sa'adah sai ji ta yi Farida ta ce "Iyah Basiru" Ranta ya yi mugun 'baci, tunda da izgilanci ta fada mata, take ko ta 'daga murya ta fara mata sababi, saboda Sa'adah mafadaciya ce ta gaske, sai dai kuma ita wacce ta yi tsokanar ta si'dade ta barta a gun. Wanda hakan da ta yi har ya fi wa Sa'a ciwo fiye da tsokanar da ta mata.
Shike nan sai Farida ta mayar da tsokanar ta zame mata 'ka'ida sai dai idan ba su hadu guri 'daya ba, ranar kuma a shop suka hadu ta faki ido ta galla mata harara tace, "Sa'ade gwalli"
Abinka da wanda aka dade ana tsokana kuma mai 'karancin ha'kuri sai kawai ta zabura ta kai mata wawura, ta sha'ke ta da 'karfin gaske, nan da nan hankalin mutanan gun ya kai kansu, aka taru aka karbe Farida a hannunta, tana mayar da numfashin wahala dan ba 'karamin sha'ka ta sha ba, musamman da ke ba ta da da kuzari saboda rashin cikakkiyar lafiya.
Aunty Ngozi malamar (Mathematics) ce ta zo wucewa ta tsaya tana tambayar ba'asi, bayani aka mata wanda kusan duk gurin shaida aka wa Farida cewa tana tsaye kawai aka ga Sa'adatu ta kama ta da kokawa.
Saboda haka sai ta tattara su ta tafi da su Staffroom wanda a can aka yi shari'a. Kusan dukkan staff din bayan Farida suka bi, saboda rashin hayaniyarta, ga ta kuma hazi'ka ce, haka aka yi punished din Sa'adah ta hanyar sa ta shara da kuma gargadi mai tsanani, akan komai za a mata ba ta da ikon daukar doka a hannunta.
Hatta Uncle MK, Sa'adah ya jawa kunne akan zai yi wahalar gaske Farida ta tsokane ta wanda hakan da yayi yasa ta jin wani takaici ya kama ta fiye da yadda aka ba ta horo bayan kuma ita ce da gaskiya. Wannan abin ya yi matu'kar tsaya wa Sa'adah a ranta, shi yasa ta ji gaba'daya makarantar ta fita akanta musamman ko yaya idan ta ga gilmawarshi da Farida sai ta ji dukkan walwalarta ta kau, duk da dai ba ta da tabbacin abin da take zargi a tsakanin su.
Tunda ga nan kuma Farida ba ta sake marmarin tsokanar Gogel ba dan kuwa ta ji 'kamshin mutuwa a hannunta🤩.
Ana cikin haka aka fara register din JAMB, tana fada wa Baffan su maganar kai tsaye ya ce mata ba wata jarrabawar shiga Jami'ar da za ta yi don kuwa aure zai mata idan mijin ya yarda sai ya siya mata ta yi a 'dakinta.
Wannan ma na cikin damuwar da ta sake sa mata tsanar FGC KANO. Dukkan 'yan ajinsu za su yi wannan jarrabawar sai ita kadai ce a ajin za a ce ba za ta yi ba. Wanne irin koma baya ne wannan? Wannan ba da kai har ina? Kamarta ace ita ce koma baya a komai?🤔 Sa'adah ke nan!
Wadannan damuwowin sai suka sa ta ji gara ta koma asalin makarantar da ta bari a baya ta zana jarrabawar kammala sakandire, nan ma da ta gabatar da maganar gaban Baffa tare da ba shi uzirin ai ba sosai ake cin jarrabawa a wannan makarantar ba, kai tsaye ya ce mata bazai yiwu ba, tunda anriga an biya mata kudin jarrabawar ba, ba za a yi asarar su ba, wannan shi ne karon farko da Baffan bai goya mata baya akan wani abu ba.
Ganin ba ta sami goyon baya ba, ga kuma ba'kin cikin da za ta kwasa a FGC KANO, sai kawai ta daina zuwa makarantar gaba'daya, wanda hakan bai damu Baffanta ba, sai cewa ya yi to ta fito da miji, ai Sumayya ma ba ta sami hakan ba ya aurar da ita ga shi nan kuma tana zaune lafiya cikin rufin asiri mai yawa, fiye ma da wanda suka yi karatun.
Inna kuwa uffan ba tace mata ba saboda yadda take ganin take-taken Sa'adah nan gaba fin 'karfinsu za ta yi, garama a aurar da ita ya fi mata kwanciyar hankali.
Tsawon sati tana gida ba ta je makarantar ba, rannan da yamma tana kwance a dakinta, tunda yanzu Inna fushi take da ita sosai, don haka ba ta jin da'din zaman gidan gaba'daya, ta ji murya Baffa na fadin"Iyah"
Da sauri ta amsa ta fita tsakar gida inda yake tsaye, ta tsugunna tare da cewa "Gani Baffa"
Ya kalle tay ya ga duk ta lalace tsabar fitinar da ta sawa ranta.
ya ce, "Da ma yaron nan Mutari ashe a makarantarku ya ke koyarwa?"
Shiru ta yi tana nazarin sunan, kafin ta ce, "Wani abu ya sake cewa?"
"Dazu ya same ni a inda nake zama shima nan ne wajen zamansa ya tambaya an tabbatar masa nan ne gidan ku, ya yi mamakin yadda, bai gane ke yarinyar wajena ba ce sai a kwanakin nan, kuma ya ga ba kya zuwa makaranta shine ya tambaya lafiya kuwa?"
Ya nisa sannan ya ci gaba da fadin, "Na fada masa kawai makarantar ne ba kya so, ni kuma ban takura miki sai kin ci gaba da zuwa akan dole ba, amma ba zan zauna na zuba miki ido ba, aure zan miki!
Ya ro'ke ni alfarmar yana son ya zo ya ganki ya ji dalilinki na gudun makarantar alhalin aski ya zo gaban goshi, na amince masa ya zo ba dan komai ba, sai don mutuntani da yake yi, katifar ma da kike kwana a kai shi ya kawo miki ita, don haka idan an yi sallama da ke bayan La'asar na miki izinin ku tsaya a zaure"
Kai ta 'daga tare da cewa
"To"
ya juya ya fice ita kuma ta koma daki tana jin faduwar gaba.
'Karfe hudu da rabi 4:30pm yaro ya shigo ya ce, "Wai ana sallama da Sa'adatu" Daidai lokacin ta fito a ban'daki dan haka ta ce, "Je kace tana zuwa".
A gurguje ta shirya cikin tsadaddiyar doguwar riga Coffee Colour ta yi roling da mayafin rigar, ta fesa turare bayan ta shafa powder da wet lips, ba ta cikin walwala don haka ba ta sami sukunin yin kwalliya sosai ba, duk da hakan rigar ta karbe ta, ta yi mata kyau.
Dakin Inna ta le'ka ta ce mata, za ta fita." Kai ta 'daga mata ita kuma ta dauki 'yar 'karamar tabarmar da take jingine a dakin ta fita.
A jingine ta same shi, ya yi shigar 'kananun kaya, wandon jeans ne mai kalar ba'ki, sai T-shirt fara 'kal an rubuta *PYRAMID* da manyan ba'ki a gaban rigar, zanen dutsen pyramid 'din kuma ta bayan rigar, 'kafarsa dauke da boot farare sai zabga 'kamshinsa na dindin yake yi, sumarshi tasha gyara sai she'ki take yi, yau har farin glass ya saka wanda ba kasafai yake amfani da shi ba, ba ta yi mamakin shi ne Mutarin da Baffa yake bayanin sa ba, saboda ai ya taba ce mata yasan Baffan shi ma.
Ba 'karamin kyau ya mata ba, amma da yake haushin sa take ji sai bai wani burge ta ba, sai da ta shimfida tabarma ta ce "Bismillah!" Ta juya ta dauko ruwa, a zaune ta same shi a farkon tabarma ita kuma ta sai ta zauna a 'karshen tabarmar.
Da 'kyar ta bude baki ta gaishe shi, ya amsa yana nazarin yadda ta zabge lokaci guda.
Kai tsaye ya ce, "Mai ya hana ki zuwa makaranta tsawon sati guda?"
Shiru ta yi amma a zuciyarta fadi take na bar muku makarantar sai ku tabbata kai da Farida da sauran staff masu shaidar zur, har Mahdi ya bayyana.
Sau biyu yana tambayar ta, ba ta 'dago kanta ba, bare ta amsa mishi. A karo na uku ya yi magana a kausashe tare da cewa "I will not repeat myself!"
Cikin turo baki ta ce "Ni ban son makarantar ne na gaji"
Mamaki ya kama shi wacce irin yarinya ce wannan? Ka zo shekarar 'karshe a karatunka kuma rana daya ka ce wai ka gaji?
Ya zuba mata ido yana nazarinta matsakaicin tsayi gare ta, ba'ka ce amma ba sosai ba, irin su ake cewa wankan tarwa'da, zagayayyiyar fuska ce da ita, mai dauke da manyan idanuwa dara-dara, gashin girar ta a cike, sannan hancinta ya dace da fuskar sai dan 'karamin baki irin na Baby Girl🤩, mai dauke da wushiryar da take 'kawata murmushinta, ga ta kuma da dimples a dukkan kumatunta ko motsa bakin ta yi sai sun lotsa, ba siririya ce ba amma kuma bata da jiki na sosai, sai dai a cike take, 'kasanta ne mai fadi, amma ta sama a tsuke take musamman da ta yi sa'a ba ta da tumbi sai hakan ya taimaka wurin fito da cikakkiyar sura mai birgewa. Shi yasa uniform ke mata kyau tunda sai sun mishi shape sannan kuma hijabin su 'dan mitsil ne.
Ya nisa yana kokawa da zuciyarshi, ya ce, "Ban gane kin gaji ba"?
Shiru ta yi ba ta ce 'kala ba.
Ganin yadda ta rame ya san dole akwai wani abu daya sata wannan borin sai ya tausasa murya ya ce,
"Sa'adah what's your problem, mai yasa haka? Ba za ki ji tausayin iyayenki ba, duk wahalar da suka yi sai da abu ya zo gaf, kice ke ba za ki yi ba, ko auran kike so wata nawa ya rage ki kammala sai a miki"
Wani malolon ba'kin ciki ya tokare mata wuya, tasan Baffa ne ya ce mishi haka, ta kasa magana amma ranta in ya kai dubu to ya baci.
Sai shi ne ya gaji da shirun ya ce, "Tunda gajiya ce kawai dalilinki ai yanzu kin huta tunda kin fi sati kina hutawa, kuma gobe Monday lallai ki shirya ki zo makaranta.
Kai tsaye ta ce, "Idan har FGC ne sai dai a kai gawata!"
Ta fada kuka na kwace mata, ta sunkuyar da kai tana danne kukan.
Shiru ya yi tare da tunanin dalilin 'kin makarantar haka farat 'daya, murya ba amo ya ce "Listen, idan aka canja miki wata makarantar za ki je"?
Kai ta 'daga mishi.
Ya ce "it's ok but let's talk the reality. Fada mini dalilinki na son barin makarantar ni kuma idan na ji kina da hujja da kaina zan nemo miki wata makarantar na kawo wa Baffa"
Ta yi shiru sai shesshe'kar kuka take yi, jikinsa ya yi sanyi zuciyarsa sai kisima mishi abubuwa take yi.
Ya dade yana lallashinta da kalmomi masu dad'i har ya samu ta bude baki ta ce, "Akan me zata dinga tsokana ta sannan duk a hadu a ba ni rashin gaskiya? Saboda ita Babanta mai kudi ne, ni kuma nawa talaka? Saboda ita mai haza'ka ce, ni kuma ba ita ba ce? Duk staff kowa ita ya gasgata! amma ni da nake yar class 'dinka, ka kasa kare mini hakkina, saboda ita Bebinka ce, ni kuma ka tsane ni? To na bar mata makarantar ta tabbata a ciki kar ta fita"
Mamaki ya yi matu'kar kama shi amma ganin ta hau dokin fushi mai yawa, sai ya tattaro dukkan alhini ya ya'ba a fuska da gangar jikinsa.
Ya kira ta, ta amsa ba tare da ta 'dago kanta ba, cikin muryar lallashi ya ce, " Have I ever said I hated you?"
Ta girgiza kai alamun a'a sai kuma ta ce. "No, but actions speak louder than words!"
A thick silence sweeps the atmosphere! Ya zama speechless, bai yi tunanin irin kallon da take masa ba kenan. Cike da ta'ajibi ya ce,
"Kar fa ki zama cikin jerin mutanen da idan an musu gyara yake zama gaba, tunda haka ne na miki al'kawarin ba zan sake shiga cikin case 'dinki ba, wannan bai kai dalilin da za ki bar karatu ba, sai dai idan da gaske auran kike so, ko kuma ba gaskiyar maganar kika fada mini ba."
Ta yi shiru ya ce, "Yanzu kin ha'kura za ki koma?"
"Amma ai cewa ka yi idan na fada maka dalilina za ka samo mini wata makarantar."
"E na fadi hakan! €amma nima sai da nace idan na ji kina da dalili, to ban gamsu da wannan dalilin ba."
Ta yi 'kasa da kanta,"Ai dama na san ba zaka mini adalci ba, tunda abin ya shafe ta."
Ido ya zuba matat kamar kishi take da Farida, amma kuma ai shi ba wacce ya ce yana so a cikinsu, daga Ubangiji sai shi sai zuciyarshi su kasan me yake ciki.
"Wai ta ina ta zama Bebina?"
Da sauri ta ce, "Saboda kullum bakinka baya gajiya da ambaton ta, duk fadin makarantar nan da ita kake misali, alhalin ba ita ce kawai daliba mai 'kwazo ba, sannan za ta tsokane ni, amma har da kai a masu gaskata ta, ni kuma a 'karyata ni" Ta fada cike da takaici kwarai da gaske.
Ya nisa, "To ai nace ba zan sake shiga case din ki ba"
Ya sake sassauta murya ya ce "Sa'adah!" Har cikin jikinta sai da 'kiran ya ratsa, jikinta ya yi sanyi, ya sake kiran a karo na biyu. "Sa'adah!"
Ba ta amsa ba amma ta dago ta zuba mishi manyan idanuwanta da sukayi ja saboda kuka.
"Idan na ce ke ce Bebin nawa fa?"
Da sauri ta yi 'kasa da kanta saboda yadda maganar ta dirar mata a ba zata! kuma yanayin sa ya matu'kar sa kunya ta kama ta.
"Ki dago ki amsa mini." Ya fada murya ba amo.
Ganin ta kasa magana, ya fara gaskata zarginsa na ita ma tana son sa, ya nisa tare da cewa. "Ban so na fada miki sirrin zuciyata yanzu ba, na so sai kin kammala karatunki, sai na zo na nemi aurenki a gidanku, amma ke na lura gaba'daya kallon wani 'dan ta'adda kike mini, idan za ki yarda da ni, ni ba son Farida nake yi ba, amma na san ina tausayin ta, sannan idan ke ba ki amince mini ba, to tabbas zan iya maye gurbinki da ita"
Wani takaicin ya sake kama ta akwai alamun tausayin nan zai iya rikidewa zuwa soyayya kamar yadda Zainab Ma'aji ta hasaso, abin da take ayyanawa a ranta ke nan.
Ya gaji da jiran amsarta ya ce, "Kin yi shiru?"
'Kasa ta sake yi da kanta cikin fushi ta amsa, "Tunda har za ka iya maye gurbina da ita, kawai ka ri'ke ta tun yanzu ai dama ita ce a ranka."
Ta fada murya na rawa.
"Wai ke kam wacce irin yarinya ce mai 'karyata na gaba da ita? Kin sa na fada miki sirrin zuciya ta, amma kina 'karyata ni. zan maimata miki a karon 'karshe, ke ce Bebina ba Farida ba, da gaske auren ki nake son yi, don nan ba gidan da zan yi wasa ba ne".
Ya mi'ke yana sa takalmi, yana ci gaba da fadin,
"Idan kin amince kin kuma gaskata ni, to lallai gobe na gan ki a makaranta, zan kuma fada miki wata magana. Rashin zuwan ki amsa ne na baki amince da soyayya ta ba, ba kuma ki gaskata ni ba, kin ga ba zancen ki ji ma maganar da zamu yi, zan tafi sai yadda hali ya yi ki gaida Inna!"
Ya juya ya fice.
Alkalamin
SURAYYA DAHIRU.
✍🏼✍🏼