KUSKURENA YA YIN DA NAKE ALWALA 10

*KUSKURENA YA YIN DA NAKE*
                *ALWALA*



🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬

*FUTOWA TA 👇*
           *(10)*
  
*FUSKANTAR ALQIBLA YAYIN FITSARI KO BAYAN GIDA*

 Hadisi daga Abu huraira yana cewa farin jakada babba dan Abdullahi Muhammadur rasulullah saw yace "Idan dayanku ya zauna zai biya buqatarsa kada ya fuskanci Alqibla ko ya juya mata baya". Malamai sun qaru juna sani dan gane da wannan hadisin kusan maganganu guda takwas 8 Amma magana mafi rinjaye da inganci shine abun da yazo a hadisin Abdullahi bn umar yake cewa "Na kasance wata rana akan dakin "yar uwata Nana hafsa Allah ya qara mata yarda sai naga manzan Allah saw yana biyan buqatarsa yana fuskantar shaam yana juyawa ka'aba baya "jama'a da yawa sun rawaito wannan hadisin Imamush shaukani yana fada acikin littafinsa NAILUL AUDAR yace wannan hadisin yana nuna halaccin mutum ya biya buqatarsa acikin ban daki ko zagayayyen waje ya fuskanci Alqibla ko ya juya mata baya babu laifi agaresa amma akasin haka an kyamaci mutum ya aikata hakan sai dai ya kalli kudu ko arewa.

🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬

*MU HADU A FUTOWA TA 11*

*Rubutawa... ✍️✍️✍️✍️✍️*
             *Dalibi mai neman ilimi Nazifi Yakubu Abubakar*
             *(Abu Rumaisa)*
          🥏08145437040🥏
Post a Comment (0)