JAGORANCIN MUSLUNCI DAGA JIYA ZUWA YAU // 08

JAGORANCIN MUSLUNCI DAGA JIYA ZUWA YAU // 08
.


BANU ISRA'ILA
Inda a ce banu Isra'ila mutane ne tsayayyu a kan addini ko bauta da ba su sami tangarda a kan aqidarsu ba ko kadan, domin bayan dawowar Musa AS daga Madyan ne suka ga ayoyinnan guda 9 wadanda za su tabbatar da ajizancin kowa in ba Allah ba, a gabansu ake neman Musa AS da ya roqi Allah don a sami mafita bayan ga Fir'aunan a garin, kuma Musa AS ya yi roqon Allah SW ya yaye masifar a sami mafita:-
1) Ya zo da sandar da ta riqa rikida tana zama macijiya, ta hadiye komai kuma ta koma yadda take ba tare da an ji wani tudu a jikinta ba.
.
Mutane da dama sun yi imani da Musa AS a dalilin wannan sandar.
2) Hannu: Ya riqa sa hannunsa a hantsarsa ya fito shi fari sal sai walwalniya yake yi, don dai ya nuna musu cewa yana dauke da wani saqo daga inda ya wuce tunaninsu.
3) An yi musu ruwan dufana, wanda ya shiga musu ko'ina, sai da suka nemi ya roqa musu Allah a janye musu.
4) Zaizayar qasa da suka yi ta fama da ita, wace ta addabi gonakinsu, a qarshe sai da Musa AS ya roqi Allah.
.
5) Sai kuma fari, wato qaranci ko daukewar ruwan sama, shi wannan sun kwashe shekaru suna fama da shi, sai da aka roqa musu, duka dai banu Isra'ila suna kallo.
6) Sun yi fama da fari wadanda suka riqa cinye musu amfanin gonan, suka illata musu 'ya'yan bishiya, nan ma sai da aka roqa musu.
7) Sai kwadi da suka addabe su, ko ina ka shiga sai kwado, bar wuraren kwanciyarsu hatta abincinsu tsalmawa suka riqa yi, shi ma suka nemi a roqa musu bayan ga Fir'aunan yana da rai suna gani, wannan bai sa sun yi imani ba.
8) Qwari da suka dame su, dan abincin da suka kawo gida qwarin suka bi su suka la'anta, shi ma an yi addu'a anan.
.
9) Sai babbar ayar wato tsagewar tekun Maliya inda ya rabu biyu su kuma Mutanen Musa AS suka bi shi, Tarihi ya nuna cewa Fir'auna ya bi su Musa AS a kan kekunan dawaki ne, wasu a qasa, shi ya sa tafiyar ba ta yi sauri ba domin mutanen Musa AS a qasa suke, kuma hanyar da suka biyo tuqewa za ta yi saboda teku don haka ba wani abin gaggawa ba ne, da a ce ta Suwais suka bi to da za su iya shiga bigire mai tsarkin da aka yi musu alqawari, wato inda Musa AS ya taba zuwa kenan bayan ya baro Madyan da iyalinsa, duka dai tsakanin Palastine ne da Jordan, za a iya zuwa ba sai an bi ta ruwa ba.
.
Da yake Allah SW ya yi niyyar yanke hukuncinsa a kan Fir'auna sai suka biyo ta Arewa da Sina, wato ta qasan Suwais inda in suka tsallake ruwan za su fito ta inda Tabuka take kenan a yau, wato qasar Saudia kenan, ba shakka wannan wuri ko tun farko yana hade ne da Madyan, bayan wannan lokacin ma yana qarqashin hadaddiyar daular Rum ne, a zamanin Annabi SAW ne aka fara gwada musu cewa wannan wurin ya fi qarfinsu, to Tabuka kenan dake cikin Saudia a yanzu bare kuma qasashen Sham.
.
Wadannan ayoyi da Musa AS ya riqa nuna wa Fir'auna da mutanensa a gaban banu Isra'ila ne, suna da tabbacin cewa in sun shiga wannan tekun ma ba abinda zai same su, haka suka kutsa cikin ruwan, isowar Fir'auna da yadda ya ga wurin ba zai iya komawa ta SIna inda ba ruwa ba, don in ya ce zai yi haka Annabi Musa AS da sauran banu Isra'ila sun tsira kenan, don sai ya koma sama ya zagayo ya sake gangarowa, ba zai iya riskarsu ba, sai ya kutsa kai da nufin isa inda suke cikin gaggawa, anan ne Allah SW ya halakar da shi da mutanensa gaba daya.
.
Bayan wasu 'yan kwanaki aka fito da gawawwakinsu don su zama aya ga kowa, cikin wadanda za su dauki darasi har da banu Isra'ila din, sai dai dan adam mai yawan mantuwa ne, bayan hayowarsu ne fa suka riqa samun Manna da Salwa, wato darba da 'yan tsakin salwa, lokacin da suke buqatar tausayawa ne, wannan ya faru ne na dam lokaci bayan sun hawo teku, ba lokacin da suka yi ta shawagi a sararin saharar Sina na tsawon shekara 40 kamar yadda wasu masu laranta tarihinsu suke cewa ba, shawaginsu na Sina kam ladabtar da su Allah ke yi ba maganar manna da salwa zahirin magana ma tarihi ya nuna ba Musa AS a wannan galeletuwar ya koma ga Allah.
.
Anan dai bayan sun hawo teku baqi ne matafiya wadanda suka fito ba shiri ko guzuri, ba su tanaji komai ba, sai Allah SW ya tausaya musu cikin ludufinsa, amma saboda dan adamtaka sai suka ce {Musa mu fa ba za mu iya haquri da abinci daya ba, roqa mana Ubangijinka ya kawo mana abinda qasa ke fitarwa na tsiron dake bin qasar (Kamar latas da fijil da sauranransu) da masu kama da kokomba da dangin wake, da albasa da adas} Baqara61. Wannan shi ne abincin da suka saba ci a Masar, ai kuwa sai aka ba su aka dauke manna da salwar.

Rubutawa:- Babban Manar Alqasim 
Gabatarwa:- Yusuf Ja'afar Kura

Daga 
*MIFTAHUL ILMI*

ZaKu iya Bibiyar Mu a 
Facebook⇨https://www.facebook.com/pg/Miftahulilmi.ml

Telegram⇨https://t.me/miftahul_ilmi

WhatsApp⇨ https://wa.me/2347036073248
Post a Comment (0)