MUGUN ABOKI 06


*MUGUN ABOKI...................*

👬👬👬👬👬👬👬👬👬👬👬

             *FUTOWA TA👇*
                     *(6)*



*WASU DAGA CIKIN AYOYI DA HADISAI DA SUKAI MAGANA AKAN ABOTA DA MUTUMIN KIRKI*


    Allah subhanahu wata'ala yana fada cikin suratu zukhruf aya ta (67) 
*(الأخلاء يومئذ بعضهم لبعض عدو إلا المتقين)*
Masoya a wannan yinin (ranar alqiyama) sa shinsu zai zama maqiyi ga sa she sai dai masu taqawa. 
قال تعالى على لسان الكافرين : *( يا ويلتى ليتني لم أتخذ فلانا خليلا) الفرقان 28*
Haka Ubangiji subhanahu wata'ala yana fada akan har shen kafirai " Ya kaicona ina ma ace ban riqi wane a matsayin aboki ba"

    Wannan ayoyon na nuni qarara cewa har a filin alqiyama abota zatayi tasiri, amma abotar da aka ginata bisa tafarkin Ubangiji ita ce zatayi nasara. 

Haka farin jakada babban dan Abdullah Muhammadurrasulullah saw yana cewa : 
*( لا تصاحب إلا مؤمنا،ولا يأكل طعامك إلا تقي)*
"Kada kayi abota sai da mumini, kada wanda yaci abincinka sai mai tsoran Allah". 

Ya qara da cewa : *(المرء على دين خليله فلينظر أحدكم من يخالل)*
"Mutum yana kan addinin abokinsa dayanku ya duba dawa zai yi abota"
  Malamai sun tafi wajan tafsirin wannan hadisin akan cewa aboki na da tasiri akan abokinsa, aboki na kwarai yana koyawa abokinsa kyawawan dabi'u, haka zalika aboki na banza na koyawa abokinsa munanan dabi'u". 

Haka ya qara da cewa "Misalin zama da mutumin kirki da mutumin banza, kamar mai dauke da turaren almiskine da mai dauke da kayan qira, mai dauke da turaren almiski ko dai ya baka, ko kasiya daga gareshi ko kaji qamshi daga gareshi qamshi mai dadi, amma mai dauke da kayan qira ko dai ya qona maka tufafinka ko kaji wari daga gareshi wari mai doyi " *Muslim ne ya rawaito.*

Kwata-kwata babu Alkhairi wajan abota da mutumin banza, saboda zai cutar da musulmi ba zai taba amfanuwa da shi ba, abota dashi zata zama fitanane ga mutum a addininsa da duniyarsa, saboda haka ne manzan Allah (saw) ya tsawatar akan zama dashi kuma ya kwadaitar akan zama da aboki na kwarai



*UBANGIJI KA NISANTAR DAMU DAGA MIYAGUN ABOKAI*


*MU HADU A FUTOWA TA 07*

*Rubutawa...✍️✍️✍️✍️✍️*
        *Dalibai masu neman ilimi*
        *Nazifi Yakubu Abubakar*
         *(Abu Rumaisa)*
       🥏08145437040🥏
*MARYAM HUSAIN ABDULLAH*
       *(UMMU HANAN)*
       🥏08026799975🥏
Post a Comment (0)