MUGUN ABOKI 05

*MUGUN ABOKI...................*

👬👬👬👬👬👬👬👬👬👬👬

             *FUTOWA TA👇*
                       *(5)*



*TA YA YA ZAKA ZABI ABOKI NA KWARAI*

 Yana da kyau ka tsaya tsayin daka wajan zabar abokai na kwarai, saboda abubuwan da suka zo mana cikin littattafan tarihi akan yadda abokai suke cin amanar abokansu hakan sai ya zama izina gareka wajan tsayawa tsayin daka wajan neman abokai na kwarai da nisantar na banza. 
   Abubuwan da zaka kula dasu wajan neman abokai na kwarai sune kamar haka :

*1- Zama tare da cakuduwa da mutanan da suke kewaye da kai:* kafin ka zabi abokai abu na farko da zaka yi kasan wadanda suke ke waye da kai, misali idan kai dalibi ne yi qoqari wajan zama da Abokanka lokacin da ba'a darasi da lokacin bitar karatu, idan kuwa ma'aikacine yi qoqari wajan tarayya da su wajan tattaunawa ya yin aiki da lokacin da ba'a aiki, a haka zaka fahimci da yawa daga cikin dabi'u, da kaikawowar ko wanne daga cikinsu da matsayin halayyarsu da iliminsu hakan zai taimakamaka wajan tantance dawa zaka yi abota. 

*2- Bi sannu-sannu wajan zabin* yana da kyau kabi a hankali wajan wannan zabin, abokai suna shiga cikin rayuwarmu ba tare da mun sani ba, don haka ka kula wajan bi a hankali da taka tsantsan, kada ka yi sauri wajan cewa wane abokina ne wane kuma ba abokina bane, baya daga cikin sanin ciwan kai daga haduwa da mutum a makaranta ko wajan aiki cikin sati daya ko makamancin haka baka san ya haqiqanin dabi'a da halayansa ba ka kira shi akan ya shiga gidanka , idan ya kama hakan ka kirashi wajan gidanka, yana da kyau ka lura da hakan. 

*3- Yi qoqari wajan jarraba wanda ka ke san abota da shi* wannan gaba ce mai matuqar mahimmanci yana da kyau ka jarraba mutumin da ka ke san abota da shi ta hanyar da kaga ta dace, domin ka fahimci cewa shin ya cancanta kayi abota da shi ko a a, hakan zai taimakamaka wajan samun aboki na kwarai, 

*4- Ka kula da kaikawowarsa tare da sauran jama'a:* idan kana san sanin halin wanda ka ke san abota da shi yana da kyau ka kula sosai wajan sanin ya Mu'amalarsa take da sauran jama'a shin yana muna furcinsu ya yin da basa nan, yana fadar mummumar magana akansu ko a a, akwai abubuwa da yawa da zaka iya kula dasu wajan sanin mu'amalarsa da sauran jama'a, idan ya kasance kubutacce daga haka to ya cancanci kayi abota da shi. 

*5- Karba da girmamawa tsakaninku:* ita abokantaka tsakanin abokai alaqace wacce girmamawace ke tallafe da ita , wajibi ne ka karbi abin da abokinka ya zo maka dashi duk da yadda kuka sa6a dashi wajan addini da al'ada da wayewa, yana da kyau ka girmama tunaninsa da ra'ayinsa duk yadda kuwa ya saba da naka , sai dai baza kayi amfani dashi ba mutuqar ya sabawa addininka ko dabi'arka, duk mutumin da yake yi maka haka tabbas ya dace kayi abota da shi. 

*6- Tafiya:* tafiya tana daga cikin al'amura masu mahimmanci wanda mutum yake yi tare da abokansa, domin a tafiyane galibi kowa yake bayyana da yawa daga cikin dabi'unsa wanda a baya ba'a san shi dasu ba, a tafiyane abokai suke qarar da kwanaki masu yawa a tsakaninsu ba a wanni ba, zaka fahimci ya wane yake wajan abin da ya shafi kudi da cin abinci da tsafta , hakan zai taimakamaka wajan tantance da wa zakayi abota. 

*7- Ka kusanci wanda yake tarayya da muhimman abubuwa da ababen qauna:* mafi qololuwar abota shine kada muji kadaitaka a ko da yaushe, saboda haka yi qoqari wajan samun abokin da yake san ababen qauna da muhimman abubuwa, karatu zai iya kasancewa daga cikin ababen qauna tsakaninku, sai ku dunga tarayya wajan littattafai, haka wasan motsa jiki zai iya kasancewa, don haka yi qoqari wajan samun abokin da zai nisantar da kai daga jin kadaitaka a rayuwa. 

*8- Ka nisanci jahili:* da yawa daga cikin mutane suna fassara kalmar jahili da wanda bashi da satifiket na karatu, amma ni ina ganin mutumin da bashi da ladabi da kyawawan dabi'u da kyakykyawar mu'amala , nawa zaka samu mutum mai neman ilimi masani akan abokantaka amma kuma baya dauke da satifiket na jami'a , don haka yi qoqari wajan neman mutumin da kuke tsara ko kuma wanda ya dara ka wajan kyawawan dabi'u da wayewa tabbas zaka samu riba a wannan abokantakar.



*UBANGIJI KA NISANTAR DAMU DAGA MIYAGUN ABOKAI*


*MU HADU A FUTOWA TA 06*

*Rubutawa...✍️✍️✍️✍️✍️*
        *Dalibai masu neman ilimi*
        *Nazifi Yakubu Abubakar*
         *(Abu Rumaisa)*
       🥏08145437040🥏
*MARYAM HUSAIN ABDULLAH*
       *(UMMU HANAN)*
       🥏08026799975🥏

Post a Comment (0)