ƘADDARA A RAYUWAR 'YA MACE

KADDARA A RAYUWAR 'YA MACE.


Hausawa sukan ce, Mai rai be iya kauce wa 'kaddara.

'Kaddara wata abace a rayuwa da take zuwa a sigogi biyu, kodai ta zo ta hanyar fuskantar 'kalubale da abubuwan da zuciyata bata yi buri ba, ko kuma ta keto ta hanyar rasa abinda rai ke so ko burin kasancewa tare da shi.

Muhallin wannan rubutun akan rayuwar 'ya macene. Idan muka duba rayuwar 'ya mace musamman a irin wannan lokaci, zamu fahimci hakika suna cikin jarabawa, kowacce kuwa da sigar yadda jarabawarta take riskarta.

Sai dai kuma, ita rayuwa ta gaji hakan, mai imani baya kauce wa 'kaddara. Alkawarin Allahne sai Ya jarabce mu, domin ta hakan ne Zai gane masu imani na hakika a cikinmu.

Yā ke 'yar uwa da aure ya yi jinkiri a gare ki! Kada ki yi bakin ciki, tunda har baki iya halittan kanki ba, lallai ne baza ki iya zartas da komai ba sai abin da Allah Ya so ya faru.

Wata tana son auren amma babu masoyi, wata ga masoyan amma ba manema aure ba, wata kuma ga manema auren amma da an fara shirin aure sai komai ya rushe, wannan jarabawace 'yar uwa, kada ki zargi kanki ko ki zargi waninki, yadda Allah Ya so haka yake faruwa.

A lokacin tsanani irin wannan, so ake yi a taru a koma ga Allah, saukar da farashi be cika kawo masu saye ba, ko masu sayen sun zo baza su saya da daraja ba. Don Allah kada ki sake ki saki tufafinki na musulunci ki koma sanya gyale da sauran indecent dressing saboda ki samu mijin aure, wannan yaudarar kaine. Mai yiyuwa akwai tanadin da Allah Yake yi maki ne shiyasa ya jinkirta maki lokaci, don haka kula maza barkatai baya kawo mijin aure, hasalima hakan na 'kara nisanta ki daga mazan 'kwaraine.

Yin auren ba shi bane cinyewa, a yi aure a samu farin ciki da natsuwa shine abin fata. Mata nawane suka yi auren amma suka gwammace rayuwar gidan kurkuku a kan rayuwar auren? Mata nawa ne suka yi auren kafin shekara suka rabu? Don haka ba a yi wa rayuwa gaggawa, abi komai a sannu, hakika Allah Ya sanya kaddara a dukkan komai.

Idan kina cikin jarabawa ta rashin mijin aure, ko rashin haihuwa, ko rashin kwanciyar hankali, ki dukufa wajen tuba zuwa ga Allah tare da mayarda dukkan al'amuranki gare Shi, babu mai yaye damuwa sai Shi (SWT), ki tashi a tsakiyar dare ki roke shi Zai amsa maki.

Kada ki ganki cikin jarabawa ki yi tunanin Allah ba Ya sonkine, a'a, kowa da irin jarabawarshi, kedai ki yi fatan samun nasara a taki jarabawar.

Allah muke roko Ya wanzar da farin ciki a rayuwarmu, sannan Ya bamu karfin imanin tunkarar jarabawa.
.
.
✍🏽 Ayyub Musa Jebi.
(Ansar).

📚 Irshadul Ummah Group.
WhatsApp: 08166650256.

Join us on telegram 👇🏻
https://t.me/irshadulummah1
Post a Comment (0)