INDA KWAƊAYI DA WULAQANCI
Ya yi wujuga-wujuga duk ya fara fita hayyacinshi a wajen kokarin samo abin da zai zo gidanku jin magana, kasancewarsa ďalibin ilimi, ba lallai bane a ce yana da tarin dukiya ko wani babban aikin gomnati wanda zai dinga yi maki facaka da kuďi, amma kuma duk da haka be cire rai da yin arziki ba domin kullum yana fita neman halaliyarsa. Tun da ya fara son ki ya fara sana'a saboda a duk lokacin da aka ce ya fito a shirye, be kasance daga cikin sahun mayaudara ba, kuma ya cika sharuďďan da addini ya tsara na auras ma mutum mai addini da kyawawan dabi'u, bugu da qari ga shi yana son ki so na haqiqa, ya sha wahala a soyayyarki don ganin an rufawa juna asiri.
Ta 6angarenki kuwa, ai sam ba ki duba wannan, ke dai kawai kullum burinki shi ne ki ga mai mota ya zo, ko babban ma'aikacin gomnati, ko wani wanda zai sakar maki kuďi ki yi facaka yadda ranki ke so, wanda za ku dinga fita shopping weekly.
Irin wannan dogon buri mai kunshe da Qarancin tunani shi ne ya ja har kika kai wasu adadin shekaru ba ki yi aure ba, tun farkon tasowarki kowa na sha'awar aurenki, amma duk wanda ya zo sai ki watsa masa Qasa a ido, ai ke a tunaninki kin fi qarfinnan, irinku sai mai mota, ďan boko wayayye, Ayyah! A hankali shekaru na ta ja har Qawayenki su ka yi aure, ke kuma kin tsaya sai mai kuďi, Qannenki suka taso su ma suka samu suka rufawa kansu asiri suka shige daki, a hankali shekaru suka ja, kyawun fuskarki da surar halittarki ya fara raguwa, mutanen kirkin suka fara jin shakkar aurenki saboda tsoron bakin mutane, domin wani ma kawai dai kina kallon kankine a budurwa amma shi tuni ya yi imani da cewa kin tashi daga matakin budurci, su kuma masu kuďin a wannan lokacin Qananun tasowa suke so, don haka sai a fara kiranki da Aunty. Daga nan kuma sai duk takaici ya bi ya dame ki, ga sha'awar aure ta dame ki, ga tsegumin jama'a, ga baqin cikin ki ga Qannenki tare da yaransu, daga nan sai ki fara ramewa saboda damuwa, a nan ne asalin kyawun naki zai disashe, daga karshe sai dai a nemo wani a dangi a haďa ku ko wani wanda sam bema san Alif ba kuma ba ilimin zamanin, ko wani baqauye bagidaje. Laifin waye?
.
A'a. Wata kuwa ta samu mai kuďin, ma'aikacin gomnati ko wani babban ďan kasuwa, duk abin da take so shi yake yi mata, ya zubar wa da iyayenta da kuďi, amma kuma gare shi ba ilimi da tarbiyya irin ta addini, tun kafin aure kun gama sheqe ayar ku, a haka dai har aka ďaura aure ya kawo ki gidansa. Babu rashin ci ba rashin sa, ba rashin sutura, amma ke kenan cikin tashin hankali, wulaqanci iri-iri, ya ďauke ki tamkar house maid, ba ya ganin girman iyayenki, babu fira mai daďi tsakaninku, sam be ďauki da muhimmanci ba, da kin yi magana ya ce in kin gaji ki tafi gidanku dama kwaďayi ya kawo ki. In da kwaďayi da wulaqanci, ga ki a cikin daula amma ba ta yi amfani ba, duk kin qare kin tsomake saboda rashin natsuwa da kwanciyar hankali. Wannan shi ne abin da ke damun dayawa daga cikin mata a wannan zamani.
Su kuma iyaye, dama tuni su suka tarbiyantar da yaransu a kan kwaďayi da dogon buri, ba su ba su tarbiyyar da ya dace ba, kuma sai su iyayen suka koma su ne 'ya'yan, duk abin da yaransu suke so shi ake yi whether good or bad. Irin wannan ni ya kai su ga da-na-sani. Domin duk wanda ya hau mota a tashar kwaďai, za ta sauke shi a tashar wahala.
Nasiha ta gare ku 'yanmata shi ne, ki cire kwaďayi da dogon buri a zuciyarki. Idan mai addini da kyawawan dabi'u ya zo, kuma aka samu ba zauna gari banza bane, ma'ana yana yin wata sana'a, to ki aure shi, wannan shi ne zai zama alkhairi a gare ki, amma idan kika tsaya neman kyale-kyale, Lallai ba za ki gaji da ganin abin takaici ba.
Allah Ya haďa mu da abokan zama nagari.
.
Qaninku:
✍🏿Ayyub Musa Giwa.
(Ansar).
03-03-2019.