YADDA AKE ZAKKAR NOMA

YADDA AKE ZAKKAR NOMA


Tambaya
Assalamu Alaikum wa Rahmatullah, Malam Ataimakamin da fatwa akan ko Akwai fidda zakka ga wanda yayi noma na hatsi kaman shinkafa ko masara.Shin shima zai fidda Zakka akai idan yakai nisabi?

Amsa 
Wa alaikum assalam wa rahmatullhi
Allah ya wajabta zakkar noma a Aya ta (141) a cikin Suratul An'am.
Annabi (SAW) Yana cewa "Babu zakka a cikin abin da bai Kai Sa'i 300 ba).

Idan mutum ya samu Sa'i 300 na shinkafa ko masara ko wani abincin da za a iya ci a rayu kuma zai ajjiyu, zai fitar da Sa'i 30, duk abin da ya karu akan haka to za a kasa gida goma a fitar da Kashi daya.

Duk Wanda ya fitar da zakka tabbas ya raba kansa da Sharrin da yake tare da shi, Wanda Kuma ya hana ya zuba a rumbu ya boye, Àllah zai mayar da ita miciji maikora ya sare shi ranar Alkiyama, Kamar yadda ya tabbata a hadisai ingantattu .

Allah ne Mafi sani

Amsawa.. Dr. JAMILU YUSUF ZAREWA

9/11/2021

Miftahul ilmi 
Facebook ⇨https://www.facebook.com/Miftahulilmi.ml

TELEGRAM ⇨https://t.me/miftahulilmii

WhatsApp⇨ https://wa.me/2347036073248
Post a Comment (0)