YAUSHE AKE BIYAN WANDA YA YI AIKI LADANSA?



YAUSHE AKE BIYAN WANDA YA YI AIKI LADANSA?

Tambaya:
Assalamu alaiakum Malam idan ka bawa mutum aiki yaushe ya kamata ka biya shi ladan aikinsa ?

Amsa:

Wa alaikum assalam Ana biyan mutum ladansa daga zarar ya gama aikinsa, Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yana cewa : "Ku bawa dan kwadugo ladansa kafin guminsa ya bushe" kamar yadda Ibnu-majah ya rawaito a hadisi mai lamba ta : 2443, kuma Albani ya inganta shi a Irwa'ul-galil hadisi mai lamba ta : 1498 .

Sannan Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya hana taurin bashi, kamar yadda yake cewa : "Taurin bashin mawadaci zalunci ne, yana halatta mutuncinsa da yi masa ukuba" Bukhari a hadisi mai lamaba ta : 2400.

Don haka ya wajaba mutukar yana da hali, ya biya wanda ya yi masa aiki daga zarar ya gama, kar ya jinkirta .

Allah ne mafi sani .

DR. JAMILU YUSUF ZAREWA
2/4/2014.

📚 Irshadul Ummah WhatsApp.
Post a Comment (0)