DIREBAN MOTA DA YA ZAMA SABABIN MUTUWAR MUTANE DA YAWA, YA YA KAFFARARSA ZA TA KASANCE?
:
*TAMBAYA*❓
:
Assalamu Alaikum Sheikh!!!; Mutum ne suka yi accident a cikin mota sai aka kai su asibiti, bayan wasu kwanaki wasu daga cikin wanda suka yi accident É—in suka mutu. Shin Malam mene nematsayin direban motan?, zai yi azumi ne?; kuma idan zai yi guda nawa zai yi?, saboda ba mutun daya ne ya mutu ba.
Ina fata Sheikh zai amsa don ma amfanin ragowar musulmai masu damuwa da irin wannan. Na gode Allah ya kara ilimi da imani.
:
*AMSA*👇
:
Wa'alaykumussalam
To dan uwa kisan kuskure yana wajabta abubuwa guda biyu:
1. Diyya wacce dangin wanda ya yi kisan za su bayar ga dangin wanda aka kashe da kuskure, sai dai in sun yafe.
2. Kaffara, wacce zai 'yanta kuyanga, in bai samu ba sai ya yi azumi sittin (60), kamar yadda aya ta 92 a Suratun Nisa'i take nuni zuwa hakan.
Idan sama da mutum É—aya suka mutu a mota, ya wajaba ga Direban motar ya yi wa kowa kaffara kuma danginsa su biya diyya, mutukar shi ne sababi a haÉ—arin, kamar ya zamana ya wuce danja ko kuma ya yi gudun da ya zarce ka'ida, ko burkinsa ya lalace amma ya ki gyarawa, ko wani abu makamancin haka wanda yake nuna sakacin Direba, ko wuce ka'idarsa.
Idan hatsari ya faru wasu suka ji ciwo saboda sakacin Direba ko wuce ka'idarsa, sai suka mutu daga baya, danginsa za su biya diyyarsu kuma zai yi wa kowa kaffara, ko da kuwa bayan shekaru biyar ne da faruwar hatsarin, saboda duk dalilin da yake kaiwa zuwa abu, to yana dadidai da abun.
Allah ne mafi sani.
Don neman Karin bayani duba : Al'inaya 1\116, Madalibu Uli-Annuhaa 6\147 da kuma Fataawa Allajnah Adda'imah 23\352.
Dr Jamilu Yusuf Zarewa