FALALAR RASUWAR YARO QARAMI :
TAMBAYA TA 2213
********************
Assalamu alaikum. Ina daga cikin dalibanka na zauren fuqhu. Muna godiya sosai, Allah yasaka muku da alkhairi.
Malam 'Dana ne ya rasu, yau sati daya kenan da rasuwarshi. Ya kasance tun dana haifeshi, Allah ya Dora masa jinya. Baya xama baya komai sai dai in yaji yunwa yayi kuka.
Tou malam tambayata anan itace, inason in samu yafiya tsakanina dashi saboda sometimes yaro yana kuka yanason ya ci abinci kaikuma kana wani abin, Ko kuma ka ajiye (shi) a gado ko kujera da ya fado, ranshi ya baci yayi kuka.
Tou malam zai iya yafe mun?.
Na biu kuma malam Dan Allah inason kayimun bayani akan falalar ka rasa danka yana qarami ko xan samu hankalina ya kwanta in samu natsuwa.
Na uku kuma malam jinyan nashi kamar ta mutanen boyece, anata cemin in nemi magani Dan in ba hakan ba sukan iya dawowa idan ka sake haihu, shin gaskiya ne ko kuma? Idan har gaskiya ne me da me xanyi domin in samu kariyaIn samu kariya daga sharrin su? Nagode Allah ya saka da alkhairi ya tsare mana malam
AMSA
*******
Wa alaikis salam wa rahmatullahi wa barakatuhu.
Da farko dai muna rokon Allah ya jikan Yaronki, ya rahamsheshi, ya sanyashi cikim mizaninku aranar Alqiyamah. Ameeen.
Babu bukatar neman yafiya awajensa bayan rasuwarsa. Babu abinda yake bukata daga gareku in banda kyakkayawar addu'a da kuma fatan Alkhairi.
Daga cikin falalar rasuwar yara Qanana :
Daga Sayyiduna Anas bn Malik (ra) yace Manzon Allah (saww) yace:
"BABU WANI MUSULMIN DA (YARANSA) UKU ZASU RASU, WADANDA BASU BALAGA BA, FACHE SAI ALLAH YA SHIGAR DASHI ALHANNAH DA FALALAR RAHAMARSA JIN QANSA GARESU".
(Bukhariy da Muslim ne suka ruwaitoshi).
An karbo daga Sayyiduna Abu Sa'eed Alkhudriy (ra) acikin wani dogon hadisi Manzon Allah (saww) ya gaya ma wasu Matayen Sahabbai cewa:
"BABU WATA MACE DAGA CIKINKU WACCE 'YA'YANTA GUDA UKU ZASU GABATA (WATO ZASU RASU) FACHE SAI SUN KASANCE TSARI GARETA DAGA SHIGA WUTA".
Sai wata mata tace "Koda guda biyu ma?". Sai Annabi (saww) "GUDA BIYU MA".
(Bukhariy da Muslim ne suka ruwaitoshi).
Rasuwar yaro yana daga cikin manyan musibu ga Mahaifansa. Kuma Allah Madaukakin Sarki yana bada sakamako mai girma ga bayinsa masu hakuri. Don haka kiyi hakuri ki nemi ladanki wajen Allah.
Bayan haka kuma ki yawaita amfani da Man Habbatus sauda acikin abincinki, Kuma kina yin hayaki da ita yayin da kike da juna biyu. In sha Allahu babu abinda zai faru gareki da kuma abinda kike dauke dashi.
Allah yasa adace.
WALLAHU A'ALAM.
DAGA ZAUREN FIQHU (20-09-1438 15-06-2017).