HUKUNCIN YIN ADDU'A ACIKIN SUJADDA
*TAMBAYA*❓
:
Malam mutum zai iya rokon Allah Acikin kowace sujjada ko kuwa sai sujjadar karshe ??? Sa'anan idan ya tashi rokon zai iya yi da hausa ko kuma dole sai da larabci ??? Sai kuma naji Ana cewa daga hannu bayan An gama sallah idan mutum zai roki allah kukskure ne yaya ingancin wannan zancen yake ???
:
*AMSA*👇
:
Babu laifi Acikin kowace sujjada ka roki ubangiji Abinda kake so ba sharadi bane sai raka'ar karshe.
Ya halatta mutum yayi da duk kalar yaren da ya iya don shi Allah yana jin kowane yare ba sharadi bane sai kayi da larabci, anfison ayi ne da Larabci sakamakon shine yaren da yafi kowane daraja A wajen Wanda ake rokon, amma babu laifi ayi da hausa ko wani yaren na daban duk da acikin sallah ne.
Sai kuma Daga hannu alokacin da mutum za6e roki Allah sunna ne haka aka fii so ma idan mutum zai roki Allah ya daga hannuwansa sama.
Abinda bai tabbata bah shine shafa hannuwa bayan idar da addu ar.
Babu wani ingantaccen hadisin da yazo da Annabi ya taɓa shafar fuskar sa yayin da ya gama addu'a saboda haka mutum ya shafi fuskarsa bayan ya gama addu'a bidi'a ne. Abinda ake so mutum ya daga hannuwansa sama cike da YAQININ ALLAH zai karba masa abinda yake rokon sa ya roki Allah abinda yake so bayan ya idar sai ya sauke hannun sa basai ya shafa A fuska bah
Wallahu A'alam
Attajiree
08029934447
Ku kasance damu domin ilimintarwa, Fadakarwa da Tunatarwa a Sunnah.
KU BIYOMU A TELEGRAM:👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
KU BIYOMU A FACEBOOK👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
Yaku Yan'uwa masu albarka Ku taya mu isar da wannan sakon ta hanyar SHARING wasu da yawa zasu amfana