INA DA MOTOCIN HAYA, KO YA HALATTA NA AMSHI "BALANCE" DAGA HANNUN DREBOBI KULLUM ?

INA DA MOTOCIN HAYA, KO YA HALATTA NA AMSHI "BALANCE" DAGA HANNUN DREBOBI KULLUM ?


Tambaya
Assalamu alaykum Doc, Mecece mafita ta Sharia akan balance na abin hawa da ake amsa a wajan Drebobi kullum, in an basu motar haya ko mashin su ja ?

*Amsa*

Wa alaikum assalam
A zahirin nassoshin Sharia abin da yawancin mutane suke yi a garuruwanmu bai dace da Ka'idojin Sharia ba, saboda akwai rashin tabbas da kuma garari a ciki, saboda in an samu kudi da yawa mai motar ya samu nakasu, ranar kuma da aka samu Pasinjoji kadan Driban ya cutu, tun da ba zai iya canja Balance din da aka yanke masa ya kawo ba, kaga wannan ta'amulin zai shiga cikin hanin da Annabi (S.A.W.) ya yi akan garari a cinikayya a cikin hadisin da Muslim ya rawaito .

Ingantaccen bayani a wannan tsarin shi ne wanda za'a cimma daidaito wajan bada wani sashe yankakke (Pacentage) na daga abin da Dreba ya samu kullum ko kuma duk wata, kamar ya dinga bawa mai motar rabin abin da ya samu ko kuma (rub'i) kamar yadda malamai suka yi bayani a babin Cinikayya ta hadin guiwa.

Duk da cewa wannan tsarin shi ne ya dace da Sharia, saidai yawancin Drebobinmu ba su da amanar da za su bayyana hakikanin abin da suka samu kullum, ta yadda za'a fitar da sashen da aka cimma daidaito, don haka akwai bukatar yi musu wasici da tsoran Allah, da kuma sanar da su cewa, dukiya tana albarka ne in an neme ta ta hanyar da ta dace.
Wanda ya kiyaye dokokin Allah, tabbas zai azurta shi ta inda ba ya zato !

Allah ne Mafi sani.

*Amsawa✍️*
*DR. JAMILU YUSUF ZAREWA*

10/06/2020


Domin samun fatawoyin Malam Kai tsaye sai a kasance damu a 

FACEBOOK⇨https://www.facebook.com/pg/Miftahulilmi.ml

TELEGRAM⇨
https://t.me/Miftahulilm2

WhatsApp⇨ https://wa.me/2347036073248
Post a Comment (0)