JAGORANCIN MUSLUNCI DAGA JIYA ZUWA YAU // 25
YAQIN AHZAB
Wannan yaqin kusan daidai yake da na Badar wurin a shuhura wurin mutane, ko mu ce wadannan yaqoqi guda 3 wato Badar, Uhud da Ahzan manyan yaqoqi ne masu matuqar mahimmanci, saninsu ke sa mumina ya tuno martabar sahabbai da jajurcewarsu wurin taimaka wa Annabi SAW don isar da saqon da Allah SW ya aike shi da shi ga al'umma, Badar dai shi ne mabudin yaqin, da kafurawa suka ji jiki kuma aka kashe kusan manyansu gaba daya sai hankalinsu ya tashi suka yi alwashin daukar fansa, dama can ga tabon toshe musu hanyar kasuwanci wanda shi ne ummulhaba'isin yaqin Badar, dalilai sun qaru kenan.
.
To bayan an yi yaqin Uhudu buqata ba ta biya ba Makkawa suka fahimci cewa musulmai a Madina fa sun wuce duk inda ake zato, su kadai ba za su iya yaqarsu ba, sai suka gayyaci qawayensu daga sassa daban-daban na duniyar Larabawa don su murqushe muslunci kowa ya huta, dama can yaqin Badar Makkawa ne suka bi musulmai har gidansu, da kwalliya ba ta biya kudin sabulu ba suka koma, Uhudu ma su suka sake bin musulmai, Allah ya taimake su suka kare kansu wannan na ukun ma su ne suka sake bin musulman a yaqin taron-dangi wanda ake kira shi da Ahzab ko kuma Khandaq.
.
1) Da farko dai wannan yaqin ya yi kama da na Badar, yadda Allah SW ya ga halin da muminai ke ciki agaza musu.
2) Ba a zubar da jini da yawa ba a duka bangarorin guda biyu, saboda ba a yi lafiyayyar taho mu gama kamar yadda aka yi a Uhud da Badar ba.
3) Tsoro da Allah SW ya jefa wa Larabawan.
4) Yadda sahabi Nu'aim RA ya sami damar raba kan taron dangin ta yadda suka kasa gasgata junansu.
5) Wata iska daga Allah wace ta qara razana su har suka tabbatar da cewa yaqin ba zai yuwu musu ba suka watse.
6) Bayyanar nasarar da musulmai suka samu a kan Quraishawa a karo na uku bayan Badar da Uhud.
.
7) Yanzu gwamnatin muslunci ta qara qarfi, domin kafin wannan yaqi na taron dangi musulmai a Madina suna qoqarin kare kansu ne, amma yanzu bayan yaqin sun sami qarfin da su kansu za su iya kai farmaki wani wuri, wannan shi ne fassarar maganar Annabi SAW da yake cewa: "To yanzu fa mu ne za mu yaqe su ba su ne za su yaqe mu ba, za mu bi su har makwancinsu" (Buhari, Kitabul magazi, babu gazwatil khandaq, 5/58, lamba ta 4110).
8) Wannan yaqin ya tono qulumbitar da Yahudawan banu Quraiza ke qullawa ta tarayya da Larabawan Makkah, hakan kuwa babban lefi ne na warware wancan alqawari da aka ambata tun farko, ko wannan sun cancanci hukunci.
.
9) Wannan yaqi ya bude qofar da musulmai za yaqi banu Quraiza.
10) Yaqin qarshe kenan tsakanin Makkawa da Musulmai a Madina. Amma sahabin da ya wargaza kan mayaqan shi kadai da yardar Annabi SAW a babin yaqi dan zamba shi ne Nu'aim bn Mas'ud, ya muslunta mutanensa ba su sani ba don haka ya sami banu Quraiza ya ce musu "Kun fa san ku a Madina kuke, in yaqinnan ba a ci nasara ba Quraishawa arcewa za su yi qasarsu su bar ku da Musulmai, don haka ku nemi manyansu guda goma-goma a Makka da Gatafan da sauran masu tsaya musu kamar Najad, koda yaqin ya rincabe ba su da damar tserewa su bar su".
.
Banu Quraiza suka jinjina wa fahimtar, Nu'aim RA ya lababa zuwa Makka, ya sami Quraishawa ya ce musu "To fa kun san banu Quraiza ba mutane ne da za a ba su aminci ba, tuni ma sun aika wa Muhammad da takardar sulhu, tare da alqawarin za su kawo masa mutum goma-goma daga kowani bangare ya sassare kawunansu a wuce wurin, Muhammad kuma ya yarda, don haka in sun aiko neman wadannan mutanen kar ku bayar" Ilai kuwa sai ga Yahudawan banu Quraiza na neman Quraishawa da Gadafan da sauran qabilun da su ba su mutum goma-goma cikin manyansu da za su yi jingina da su.
.
Su kuma suka tuno maganar Nu'aim suka hana, da Yahudawan suka ga an hana sai suka tabbatar da maganar Nu'aim RA, ma'ana duk bangarorin suka shiga shakkar juna, wannan ya taimaka matuqa wurin wargaza kansu, ba don haka ba da za su kware wa musulmai ne baya yadda za a ci su da yaqi, irin abin da ya sami banu Qainuqa kokadan bai zama qalu-bale ga banu Quraiza ba, ya bayyana kenan qarara cewa wadannan mutane ne da ba za a taba ba su aminci ba ko alama, dama suke nema ga musulmai, kuma duk lokacin da suka same ta ba za su taba daga musu qafa ba.
.
BANU QURAIZA
Wanda bai san abinda banu Quraiza suka yi ba sai ya zaci cewa dan qaramin abu suka aikata kuma aka dauki mummunan mataki a kansu, amma zahiri mamayar musulmai suka yi a inda kokadan bai dace ba, an yi alqawarin cewa duk wanda ya hada hannu da abokan gaba to fa shi ma yana cikinsu, in Madina za ta shiga yaqi dole su ba da tasu gudummuwar, da dai sauran alqawura, sai ga su sun warware wannan alqawari ta wurin haduwa da kafurawan Makkah don yaqar musulmai, kenan su ma suna cikin yaqin ne in aka same su kashe su za a yi, kuma suka yi qoqarin abka wa matan musulmai lokacin da mazan ke bakin ganuwa a yaqinsu da 'yan taron dangi da suka zo daga Makka, suka yi qoqarin bude wata baraka wace mayaqan za su sami damar barkowa cikin Madinan dai su gama da musulmai gaba daya.
Rubutawa:- Babban Manar Alqasim
Gabatarwa:- Yusuf Ja'afar Kura
Daga
*MIFTAHUL ILMI*
ZaKu iya Bibiyar Mu a
Facebook⇨https://www.facebook.com/pg/Miftahulilmi.ml
Telegram⇨https://t.me/miftahul_ilmi
WhatsApp⇨ https://wa.me/2347036073248