SHIN KO KASAN...

SHIN KO KASAN...


Wanda ya fi kowa kudi a kasar Lebanon "Emile Baustany" ya sa an gina ma sa kabarin sa a mafi kyawun gurare a Bairut wanda aka kayata shi da tarin kayan kawa da kwalliya....

Wata rana ya hau daya daga cikin jiragen saman sa yana yawon ran gadi kwatsam jirgin ya samu hatsari ya fada cikin ruwa....an biya makudan kudade domin a gano inda gawar sa ta ke...amma abu yaci tura ballantana a binne shi a wannan katafaren kabarin na sa...sai dai kawai jirgin aka samu.

An taba yin wani babban hamsahkin mai kudi a Kasar Burtaniya..saboda tsabar bunkasar dukiyar sa har gwamnati yakan baiwa rancen kudade a wasu lokutan...

Wata rana ya shiga katon dakin da ya ke taskace dukiyoyin sa...kwatsam cikin rashin sa'a sai kofa ta rufe shi a cikin katoton dakin, yayi ihu tare da bubbuga kofar dakin koda wani zai ji ya kawo ma sa dauki ya bude kofar, amma ina..saboda girman gidan da kuma tazarar dakin daga inda mutane suke babu wanda ya ji shi.

Kuma dama mutum ne da ya saba da yawon tafiye-tafiye, koda rana ta fadi iyalan sa suka ga bai dawo ba sai suka yi tsammanin ko yayi tafiya ne kamar yadda ya saba.

A haka yai kwana Biyu ba ci ba sha....daga karshe da ya tabbatar ba shi da matsera sai ya yanka dan yatsan sa ya rubuta da jinin sa kamar haka:

"Wanda ya fi kowa kudi da tarin dukiya zai mutu cikin tsananin yunwa da kishirwa".

Sai bayan kwanaki aka gano gawar sa bayan ya fara lalacewa.

Wannan budaddiyar wasika ce izuwa wadanda suke kallon dukiya ita ce ke biyan bukatar komai.

Ka sani cewa barin duniya shine abu mafi girma da ya ke jiran mu a nan kusa, sai dai ba mu san yaushe ne ba, ko kuma ta yaya ko a'ina ba.

Mutum ya kan yi tafiya kasahse masu nisa yayi shekaru masu yawa sannan ya dawo gida..amma a duk sanda kafar sa ta haura kan layin barin duniya to shikenan yayi tafiyar da babu dawowa ta har abada😭.

Ga wani dan takaitaccen labari domin ya zamto jan hankali gare ka ya kai dan uwa musulmi:

Wani mutum ya hau motar haya sai ya ji sautin karatum Al-Qur'ani na tashi daga motar, ya tambayi mai mota, shin wani ne ya mutu ne?

Mai motar ya bashi amsa da cewa kwarai kuwa: Zukatan mu ne suka mutu.

Dan tsaya ka lura ya kai mai karatu..ka sani a halin da ake ciki yanzu haka akwai wanda ke daure a kurkkuku (magargama) ya na fatan ina ma ya samu Mus'hafi (AlQur'ani) domin ya zamo abokin hirar sa a cikin wannan duhuwar karafunan magarmar da yake, domin ya debe masa kewa ko ya samu saukin radadin kadaici da ya tsinci kan sa a ciki.

Sannan akwai mara lafiyan da yake kwance a Asibiti ya na mai fatan ina ma zai samu dama da kuzarin karanta littafin Allah....ko hakan zai zamanto waraka ga wannan ciwo da yake fama da shi.

Dungurungum din kuma a yanzu haka akwai mamacin da ke fatan ina ma ya na da damar karanta koda mafi gajartar Aya ce a cikin AlQur'ani...watakila ta zamo sanadiyyar yayewar kuncin da ya tsinci kan sa a kabari, ko kuma ta kara ma sa haske da daraja akan abin da ya aikata na alkhairi.

Ni da kai a yanzu haka da muke karatun nan...

- ba a daure mu ke a kurkuku ba.
- kuma ba a kwance muke a gadon Asibiti ba.
- har lau kuma har yanzu da sauran numfashin da muke numfasawa a rayuwa.

AlQur'ani ga shi nan a gaban mu, a cikin gidajen mu, a cikin wayoyin mu..to shin ba za mu yi amfani da wannan babbar damar da wasu suka rasa ba mu mori abin da yai saura wajen karanta Littafin Allah ba...ko kuwa jira za mu yi har sai mun shiga rukuni daya daga cikin wadancen rukunan?

Madallah ga wanda..

ba ya fatan ya zalunci kowa.

Kuma baya kin kowa.

Baya suka ga kowa.

Ba kuma ya ganin kan sa fiye da kowa.

Dukkanin mu Fatake ne (matafiya) ne izuwa Lahira..don haka mu tanadi kyakkyawa kuma ishashahen guzurin da zai amfane mu a karshen tafiyar mu.

Ya Allah ka sanya AlQur'ani ya zamo Sanyi ga zukatan mu, me debe mana kewa a kaburburan mu, kuma me ceto a ranar Lahira.

Saboda Rahamar ka da ta rinjayi fushin ka.

Allah Ne Masani
Post a Comment (0)