WAKAR AREWA MU FARKA




  Waiwaye adon tafiya @ 62

Mal Abdullahi Abubakar Lamido 

[WAKAR AREWA MU FARKA

Yayin murnar Shekara 62...Ga tunatarwa:

Rubutawar
Mal Abdullahi Abubakar Lamido
 
Noma, Kiwo da Ilimi

Shehu Fodiyo yai wasiyya 
Mai karatu daura niyya 
Ka rike wannan wasiya
Kyam da karfi ba sako-sako ba 

Tuni Fodiyo ya yi hange 
Ya fada mana don mu dage 
To Ndeme, ndure njange 
Na san fa ba ka ki fassara ba 

Ilimi kiwo da noma 
Su ya ce mu rike da dama 
Ga su nan uku duk mu kama 
Marikinsu ba zai zaman faqr ba 

Farko ya yi kira ga noma 
Yara manya duk mu kama 
Back to land shi za mu koma 
Daga yau ba za mu zam bari ba

Nomar masara da wake 
Gero acca da rakke 
In mu kai haka za mu warke 
Yunwa ba za ta mana kisa ba  
 
Mu rike noma na maiwa 
Ridi da gyada da dawa 
In da tsarin sarrafawa 
Ba ma rasa dogaro da kai ba 

Mu ci shinkafar kasarmu
Wacce mun noma da kanmu 
Mu yi packaging abunmu 
Ba ta Thailand ko ta ‘yan Japan ba 

Dankali doya da gwaza 
Tsuntsu da baru da kaza
Mu saya gun “one another”
Ba wai mu sayo wajen na can ba 

Shehu ya ce mu riki kiwo 
Wanda yai haka ya yi wayo 
Lamari nai babu wayyo 
Ba zai tosku a duniya ba 

Matukar muka kama kiwo 
Ilimi muka daina yawo 
Dajararmu fa za ta dawo 
Ba za mu zamo abin gatse ba 

Mu rike kiwon tumaki 
Da na nagge har awaki   
Rakuma kaji da doki
Mai kiwo bai rashin kwabo ba 

Wanda duk ke son ya koshi 
Ba ya son yunwa ta kar shi
To fa tilas ne ya tashi 
Noma kiwo ba zai bari ba 

Wanda ke noman abinci 
Ya saya wa kanka ‘yanci
Ya rufe kofar talauci 
Ba za ya bi masu shantaka ba

Daga nan mu kiyaye ilmu
Yara manya dukkaninmu
Mu rike hadda da fahmu 
Ba wai Arabic ya ce kawai ba 

Mu yi ilmi na Kurani
Mu yi fannonin zamani
To musamman namu karni 
Ba karni ne na jahilai ba  

Sirrin samunsa himma 
Da yawan naci da azama 
Dole ne ka jima a nema 
Ba ka je yau gobe ba ka nan ba 

Ba shi kaunar mai badala 
Don bidarsa tana da wahala 
Ilimi bai son kasala 
Ba rana dai ake sani ba 

Wajibi a lizimci Shehi
Hakuri nazari zaka’i
Guzurinka na dan mata’i
Ba za a iya shi ba shiri ba 

Sai ka sa tsarki na niyya 
Ka zamo mai yin biyayya
Da tawali’u har da kunya
Mai girman kai ba zai sani ba 

In kana neman karatu 
Ba batun barci da hutu
Ko da yaushe cikin karatu 
Nazari himma ba ka tsaya ba  

Babu ranar kammala shi 
Tun kana karami rike shi
Har ka girma kana cikinshi 
Har ran mutuwa ba ka tsaya ba

Shi sani babban rabo ne 
Shi fa gadon Mursalai ne 
Ga shi siffan khashi’ai ne 
Mai shi ba kankani ba ne ba 

Ilimi fa garkuwa ne 
Ginshiki gun ci-gaba ne 
Ga shi hasken rayuwa ne 
Mai shi ba zai zaman duhu ba 

Ilimi mai sa sururi  
Mai yi wa harkarmu tsari
Masu shi sun kama jari  
Ma’aboci nai ba zai bace ba 

Ya fi karfin masu sata 
Masani shi ke da gata 
Mai zama a cikin wadata 
Ko da ba mai kwabo yake ba  

Jahili bai san rabo ba 
Bai ji dadin rayuwa ba 
Bai ci ribar duniya ba  
Kuma bai zanto abin fahar ba 

Jahili huhu-lahu ne 
Shi hasarar haihuwa ne
Shi da babu kusan guda ne 
Nauyinsa ba za ya kai kilo ba  

Rayuwa tai babu riba 
Sai zama a cikin ukuba 
Da duhu da bakar musiba
Bai rayu cikin farin ciki ba

Sai da ilmu ake ibada 
Sharadi ne gun shahada 
Shi makami ne fa wanda 
Inda shi ba za a zam bata ba

Mai sani babban mutum ne 
Malami fa shugaba ne 
Jahili solobiyo ne 
Matsayin su daban yake fa Baba  

Ga shi Fodio yai ishara 
Ya karantar yai bushara 
Ya fada mana don mu tsara 
Mu zamo ba masu kin shiri ba 

Shehu Fodio yai jihadu
Shi da Abdullahi Gwandu
Da Muhammadu Bello su duk 
Ba su bar jama’a cikin duhu ba 

Sun yi ilimi sun karantar
Sun yi aiki sun wa’aztar 
Gun rubutu sun wadatar 
Ba su bar mu cikin rashin sani ba

Jama’a mu tsaya mu lura 
Rayuwa mu tsaya mu tsara 
Kuskure mu tsaya mu gyara 
Ba dogewa a kan bata ba 

Mu rike noma da kiwo 
Ilimi sana’a mu dawo 
Mu cire wa Arewa ciwo 
Ba fetur za mu na jira ba  

‘yan uwa mu yawaita sadaka 
Mu yi wakafi mu riki zakka 
Duk fa tarun dukiyarka 
Ba da su ne z aka lahira ba 

Kar ka yarda da masu rowa  
Ba ka yin kyauta ma kowa 
Dukiyarka kana tsarewa 
Ba zakka ba waqaf kake ba 

Ga kudi jingim a banki
Kadara ninkin ba-ninki
Amma sam babu kirki 
Baka yo zakka da saddaka ba 

Ba ka bawa talakka jari 
Ba ruwanka da son fakiri
Kamfani ka tara jari 
Ba ka sai jari na lahira ba

Taimako ba zai kadan ba 
Haka nan ba zai yawa ba 
Ba kawai sai mai dubu ba 
Ko taro ne Rabbi za ya karba  

+ + +

Ni abin da ka bani haushi
Duniya kowa kasarshi 
Ita ce alfaharinshi 
Amma ba dan Najeriya ba 

Ba shi kaunar al’umarta 
Ba shi girmama shugabanta  
Bai du’a’in ci-gabanta 
In ba tsine wa shugaban ba  

Mu rike wa kasa amana 
Mu lizimci zaman lumana 
Tausayi enďam mu nuna  
Ba adawa ko yawan kisa ba 

A cikin hakuri mu zauna
Da zumunci kar mu daina 
Dan kasa duka kar mu raina 
Mu yi alheri mu kau da gaba 

Ku mu dinga kula da beauty 
Mu mayar da garinmu city 
Kar mu zam maiseshi dirty 
Mai dauda wanda ba clean ba  

Inda duk muka dau sana’a 
Mu ka zanto masu da’a 
Rabanna zai bamu sa’a 
Ba za ya barinmu kan bata ba 

Rabbi kai ne Khaliqina 
Wahhabu kai ne Razikina 
Rahimu kai ne Rahimina 
Ba zan ki rabonka duniya ba 

Ku taya ni da addu’o’i
Rabana Ya tsaren bala’i
Ya raba ni da mai jafa’i
Da dukan sharri na masu zamba 

Abdullahi Abubakar Lamido
Gombak
09/04/20


Post a Comment (0)