HUKUNCIN JAM'I NA BIYU A MASALLACIN DA YAKE DA LIMAMI RATIBI.
*TAMBAYA*❓
:
Assalamu alaikum malam meye halaccin sabunta wani jam'i a masallaci bayan angama na farko ?
:
*AMSA*👇
:
Wa alaikum assalam, ya halatta a sabunta, hakan kuma Mustahabbi ne.
Annabi (SAW) ya ga wani ya zo bayan an yi Sallah, sai ya ce "Wa zai yiwa wannan Sadaka, ya yi Sallah tare da shi?" kamar yadda Tirmizi ya rawaito a hadisi mai lamba ta (220).
Babu hadisi bayyananne yankakke wanda ya hana maimaita jam'in Sallah a Masallaci.
Annabi (SAW) yana cewa: "Sallar Jam'i ta fi sallar mutum ɗaya da daraja (27)", duk nassin da yake gamamme ana barin shi a yadda yake sai in an samu dalilin da ya cire wani abu a cikin shi ko ya rage masa karfi .
Allah ne mafi sani
DR. JAMILU YUSUF ZAREWA