KUNDIN MA'AURATA // 09


KUNDIN MA'AURATA // 09
.
WANI ABIN DA BA MA GANEWA
Mace takan ji dadi sosai in ta ga maigidanta ya sa hannu wurin taya ta wani aiki, tabbas akwai ayyukan da matan ba sa tunanin cewa mazan za su taimaka musu, masamman ma mu Hausa-Fulani, kamar shiga kicin yayin girki, wanke-wanke, wanke wa yaro kashi da sauransu, amma akwai wasu abubuwa masu sauqi kamar gyaran littafi, kawar da wasu abubuwa irin su takalma da kujeru, a nan mace za ta ji dadin haduwa tare da mijinta wajen canja wa gadonsu wuri, ko kujerun daki, takan gaya wa mijin ga yadda take so ta yi, ta kuma tambayi shawararsa, wani lokaci sai ka ga wurin bai yi masa ba, ya kuma gaya mata tunaninsa a matsayin shawara, in ya ga ta nace sai ya bar ta.
.
Za ta nemi ya kama mata don su matsar da gadon kusa da taga, in aka matsar din kuma qila ta ga cewa ba sirri, ko dai za a iya ganinsu ko mutane su riqa jin abin da yake wakana tsakaninsu, daganan ne za ta nema a canja wurin, in ya ji haushi zai gaya mata "Na gaya miki wurin farko fa ya fi kowanne dacewa" sai ta ce "Ni dai don Allah kamamin mu gwada wancan lungun" a ganinsa wahalar da shi take yi, tunda ya riga ya gaya mata abin da ya fi dacewa, ita kuma tana ganin wannan lamarinsu ne mata, sannan zai yuwu wani wurin kuma ya fi mata, a qarshe in ta ga ba inda ya fi wurin farko sai ta ce "To mu maida shi wurin farkon mu gani".
.
Kai maigida ka yi haquri da irin wannan, maganar gaskiya tana jin dadin taimakonta da kake yi ne, in da za ka ba ta shawarar a sake gwada wani wurin a guje za ta amsa, koda kuwa ta san cewa ba zai yi ba, don tana jin dadin aikin da kuke yi tare, amma a lokacin farko da za ta ce "Ina ganin shawararka za a bi, wurin farko ya fi ko'ina" a maimakon ya dubi dadin da ta ji a sakamakon aikin da suka yi tare sai ka ji ya hau "Aikin banza aikin wofi, kin wahalar da ni ba gaira ba dalili, ai na gaya miki tun farko ba inda ya fi wannan wurin, amma da yake abu in ba wanda kika yi niyya ba banza ne, gashinan bayan wahalar da mu kin dawo kan abin da muka ce" uwargida a irin wannan yanayin haquri kawai za ta ba shi, amma zahirin gaskiya ba manufarta kenan ba.
.
GAMSAR DA ABOKIN ZAMA
Sau tari za ka ji namiji yana kukar cewa iyalinsa ba ta da godiyar Allah, duk abin da yake ba ta ko yake yi mata sam bai iya gamsar da ita, haka ita ma za ka taras tana irin wannan kukan, inda za ta riqa cewa duk abin da take yi wa mijinta ba ya gani, sai dai ta sha wahala a banza, to me yake janyo haka? Domin amsa wannan tambayar dole mu ma mu tambaye su, shin abin da take so ne yake ba ta ko abin da shi yake so, sannan ita ma abin da yake so ne take yi masa ko wanda ita take so?
.
Galibin lokuta ko kayan sanyawa maza za su saya za ka ga wanda yake so zai sayo, ba wai don ya fi kyau ba, kawai don ya fi aminci, ita kuma abu in ba yayinsa ake yi ba ba ta da buqatarsa ko kadan, shi kuma namiji abin da yake so kawai shi za a yi, misali a kwalliyar mace ba abin da yake burge shi kamar ya ga matarsa ta yi jan lalle, ta gyara shi yana daukar hankali, ita kuma sai ta kashe duk kudin da take da shi wajen gyaran gashi, hoda da sauran kayan qamshi, a qarshe ba za ta yi maganar lallen ba bare ta dan zizara, kodai ba ya ba ta sha'awa ko kuma yana daukar lokaci ita kuma ba ta da shi.
.
Kwatankwacin wannan kamar ka samo akuya ne ka soya mata nama ya ji magi da kayan qamshi, ko ka sami kyanwa ka yanka mata ciyawa mai dadin ci ga dabbobi, dukansu ba wanda zai damu da abin da ka yi, don ba abin da yake buqata ka ba shi ba, namiji da mace halittu ne daban-daban, kowa da abin da yake so, in kana son nuna wa mace qauna lura da abin da take so, haka in mace tana son namiji ya yaba wa abin da take yi dole ta yi masa wanda yake so, duk wahalar da mace za ta sha a cikin gida, in dai ba abin da yake so take yi ba duk banza ne ba zai damu ba, haka kai ma ka siyo mata wannan da wancan kana tunanin za ka gamsar da ita, amma ba ka samun damar zama da ita kuna tattauna matsalolin gida, qarshe duk kudin da za ka kashe ko godiya ba za ta yi ba.
.
Kenan akwai buqatar ma duk mu san junanmu da abubuwan da muke buqata, in mace tana samun abin da take so ba ta damu da yawansa ko qanqantarsa ba, za ta ji dadi kuma ta gode, ba za ta taba kallon wani ba bare ta yi sha'awar abin da yake yi wa iyalinsa, za ka taras da ita kullum cikin godiya, haka shi ma namijin, in dai tana yi masa abin da ya ce, ko ta ga yana so zai kasance cikin qaunarta da yaba mata.
.
Namiji yana buqatar ya ga mace tana son sa, tana jinjina wa qoqarinsa, a wannan lokacin sai ka ga ya dage yana yi mata duk abin da take so, haka ita ma mace tana son ta ga dagewar da yake yi wajen nuna mata qauna, da kula da damuwarta, da zama da ita lokaci zuwa lokaci, da yaba mata a abincin da take dafawa da adon da take yi, da ba ta dama tana halartar wasu sha'anunnuka da zumuntarta, wasu lokutan gaskiya muna da rauni wajen nuna wa iyalammu qauna, kamar yadda su ma suke jira namiji ya nuna musu, alhali su ne masu badawa ba masu karba ba, akwai abubuwa da yawa, kamar wani hoto da na ga namiji yana miqa wa mace fulawa, ita kuma tana ba shi zuciya, fassarar wannan hoton shi ne abin da ya dace a rayuwar yau.

Rubutawa:- Babban Manar Alqasim 
Gabatarwa:- Yusuf Ja'afar Kura

Daga 
*MIFTAHUL ILMI*

ZaKu iya Bibiyar Mu a 
Facebook⇨https://www.facebook.com/pg/Miftahulilmi.ml

Telegram⇨https://t.me/miftahul_ilmi

WhatsApp⇨ https://wa.me/2347036073248

Post a Comment (0)