MAGANIN DAUKEWAR SHA'AWA

MAGANIN DAUKEWAR SHA'AWA 
:


𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
ASSALAMU ALAIKUM, Malam bani da kalaman da zan ce maka sai dai ince Allah ya saka maka da nashi mafificin alkairi.
Allah ya jikan iyayanka, idan suna raye Allah ya kara musu lafiya tare da aminci, Allah ya albarkaci iyali.

Nice wacce na samu matsalar taruwar jini, Alhamdulillahi Allah ya amsa maganin da kace nayi amfani dashi. Na samu lafiya da kashi 70% kuma har yanzu ina kan amfani dashi.
Sai dai babbar matsalar da nake fuskanta shine rashin sha'awa, kimanin shekarata 2 da wattani da yin aure amma ban san wata aba sha'awa ba, idan mijina yana tare danin wallahi sai dai nabishi kawai amma banajin komai. na gode.
:
𝐀𝐌𝐒𝐀:👇
:
Wa alaikis salam wa rahmatullahi wa barakatuhu.
Da farko dai ina godiya bisa addu'o'in alkhairi da kikayi mun dani da iyayena. Allah shi amsa, ya gafarta musu tare da dukkan Musulmai baki daya.
Sannan ina yiwa Allah godiya bisa lafiyar da ya baki ta dalilin shawarwarin da kika samu daga garemu. Babu abinda zamu ce sai dai godiya ta tabbata ga Allah Ubangijin Talikai.

Bisa matsalar rashin sha'awa kuma, ko daukewarta, akwai dalilai masu yawa dake haifar da wannan. Sai dai zan takaita akan abubuwa uku kadai.

1. Sha'awa takan gushe daga jikin Mace ta dalilin wata chuta dake tare da ita. Misali kamar ciwon sanyi da sauran nau'o'in chutukan dake shafar Mata a al'aurarsu.

2. Wani lokacin idan mace tana shan wasu Kwayoyi masi karfi na asibiti sukan gusar mata da sha'awa. Misali kamar magungunan hawan jini, ciwon Sugar, Sickler, Arthritis, Asthma, da sauransu.

3. SHAFAR ALJANU : Idan mace tana da matsalar shafar Aljanu (Musamman aljanun Soyayya) sukan dauke duk wata ni'ima daga jikinta kuma su haifar mata da daukewar sha'awa, ko jin zafi yayin saduwa.
Wata ma da zarar ta kammala Jima'i da maigidanta zata rika ganin Maniyyin yana zubewa. Idan kina fama da wannan zaki iya kiran lambar mu (07064213990) domin samun shawarwari ko magani.
Shawara anan ita ce idan kina fama da wasu daga dalilan nan dana Lissafa, to lallai sai kin magance abun kafin kisha kowanne maganin don samun dawowar sha'awa din.
Amma ga wata fa'idah nan ki jarraba :

👉Ki nemi ruwan kwakwa, madara peak, da kuma ruwan Inabi ki rika sha. Domin wadannan duk sukan haddasa dawowar ni'ima ko sha'awa ajikin Mace ko namiji.

👉Ki samu shammar ki nikashi ki rika hadawa da zuma kina sha.
In shaAllah zaki samu lafiya.

WALLAHU A'ALAM

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
Post a Comment (0)