RUNDUNAR ALLAH KO RUNDUNAR SHAIDAN?? ZABI DA KANKA. .

RUNDUNAR ALLAH KO RUNDUNAR SHAIDAN?? ZABI DA KANKA. . 


Ibnu Badda Al-Akbari Allah ya masa 
rahama yana cewa "Duk wanda ya ji gaskiya sannan yayi inkarinta to wannan yana cikin masu yiwa Allah girman kai, duk wanda kuma ya taimakawa wani akan kuskure (bayan yasan kuskure yake kansa) to hakika yana cikin tawagar shaidan". 

الإبانة ٢/٥٤

Ya kai dan uwa musulmi, shin bikin kirsimeti (Christmas) kuskurene ko ba kuskure bane?? 
     Amsar guda daya ce, Wanda Ni da kai duk munsanta bama saÉ“ani akan haka cewa idan ma akwai abunda yafi kuskure to kirsimeti shine, batace, halakace, mafi muni bama musulunci bane. Dan haka kasani duk wanda ya taya kafurai murnan bikinsu to yasani yana cikin tawagar shaidan, wanda kuma munsan inane makoma na rundunar shaidan tun aduniya bare lahira. 
     Allah madaukakin sarki yana cewa acikin Alqur'ani mai girma "Ku saurara, lalle fa rundunar shaidan sune sukayi hasara (duniya da lahira)" surah Almujadala. Dan haka ya kai dan uwa sai ka zabawa kanka, a'ina kake son kasancewa, RUNDUNAR ALLAH KO RUNDUNAR SHAIDAN?? 

#Zaurenfisabilillah 


Telegram: https://t.me/Fisabilillaaah

Facebook:
https://www.facebook.com/Fisabilillaaah/
Post a Comment (0)