MAGANIN RAGE MOTSAWAR SHA'AWA

MAGANIN RAGE MOTSAWAR SHA'AWA :


TAMBAYA TA 2530
*******************
Assalamu Alaikum, Mallam inada wasu tamboyoyi kamar haka

1. kana da azumi sai kuna hira da budurwanka da kagama hiran sai kaga digon maziyyi ajikin boxers dinka, menene matsayin azuminka na wannan ranar?. 

2. Malam menene maganin rage sha'awa ?. Ina da yawan sha'awa abu kadan yeke tada mun sha'awa ko hira Mallam.

3. Mallam na gama makaranta wacce addu'ar zanyi dan nasamu aiki dawuri ?.

Nagode ataimaka a amsa mallam.

AMSA 
*******
Wa alaikumus salam wa rahmatullahi wa barakatuhu. 

Ita sha'awa sinadari ce ta musamman wacce Allah ya gineta ajikin 'Dan Adam kamar irin su barci, yunwa, kishirwa, etc. Don haka bata da abinda ke danneta sai dai idan mutum ya tarbiyyantar da zuciyarsa akan guje ma hakan. 

Kuma ita sha'awa tana daga cikin amanonin da Allah Madaukakin Sarki ya ajiye ajikin bayinsa, Kuma yayi iyakance halastattun wuraren da ake ajiye wannan amanar. Kuma yayi bayanin cewa wadanda suka kasa kiyaye wannan amanar, sakamakonsu ita ce Wuta in har basu tuba ba. 

Allah Madaukakin Sarki ya gaya ma Manzon Allah (saww) wata nasiha wacce ya umurceshi ya gaya ma muminai. Yace :

"KA GAYA MA MUMINAI MAZA SU RUNTSE IDANUWANSU KUMA SU KIYAYE FARJOJINSU, WANNAN SHI YAFI TSARKAKA GARESU.. DOMIN ALLAH MASANI NE GAME DA ABINDA SUKE AIKATAWA".

Kuma Manzon Allah (saww) ya bama dukkan Samari da 'Yan mata shawara. Yace "YAKU TARON SAMARI!! WANDA YAKE DA IKON DAUKAR NAUYIN IYALI TO YAYI AURE. DOMIN SHI (AURE) YAFI SANYA RINTSEWAR IDANU DA KUMA KIYAYE AL'AURA. WANDA BASHI DA IKO KUMA TO YAYI AZUMI DOMIN SHI (AZUMI) TAKUMKUMI NE".

To kaga dole sai ka kiyaye idanunka daga kalle-kallen haramun, ka kiyaye zuciyarka daga tunanin sa'ba ma Allah, Kuma ka shagaltar da jikinka da zuciyarka wajen yawaita azumi da sauran ayyukan bin Allah. Idan kuma kana da dama da iko to kaje kayi aure kabi sunnar Anmabinka (sallal Lahu alaihi wa aalihi wa sallam) shi yafi. 

Ba zai yiwu kana kalle-kallen abinda Allah ya haramta maka ba, sannan ka rika zargin kanka wai kana da Qarfin Sha'awa ba. Kowa da kake gani yana da ita ajikinsa. Amma tsoron Allah ne ke sanya kowa ya kiyaye. 

Daga cikin magungunan Musulunci wadanda ake amfani dasu wajen dakile SHA'AWA akwai SHAJARATU MARYAM Ke nemeta kana jikawa aruwa kana sha. Zaka samu sauki in sha Allahu. 

Mai azumin da Maziyyi ya fita daga jikinsa ba tare da motsawar sha'awa ba, to wannan babu komai azuminsa bai baci ba. Amma wanda ya janyo ma kansa motsawar sha'awa da gangan ta hanyar zancen batsa ko kalle-kallen haramun, har ya fidda maziyyi, to azuminsa ya karye kuma zai rama guda daya ne. 

Addu'ar da zaka rike babu kamar yawan Salati ga Manzon Allah (saww) da kuma wannan addu'ar wacce Anmabi (saww) ya koya ma Nana Fatimah (alaihas salam) wato :

"YA HAYYU YA QAYYUM BI RAHMATIKA ASTAGHEETHU".

Ka rika yawan yinta acikin muhimman lokutan yin addu'arka.

WALLAHU A'ALAM. 

DAGA ZAUREN FIQHU (12-10-1439 26-06-2018).
Post a Comment (0)