*SIRRIN MALLAKAN MIJINKI*
Yadda Ake Hadin Tattabara Uwar Alkawari
Yar uwa Masana sun tabbatar cewa hadin da ake amfani da shi da naman Tantabara, babu shakka yana dadewa a jikin mace.
Zaki nemi kayan hadi kamar haka;
* Tantabaru (Mace da Namiji)
* Habbatus-Sauda (cokali biyu)
* Garin Raihan (Cokali hudu)
* Ridi (Cokali uku)
* ‘Ya’yan Zogale (daidai misali).
*Bayan:* Zaki gyara tantabarunki sai ki hada wadannan kayayyakin, sai ki dora a wuta, amma kada ki saka gyararrun Tantabarun tukunna. Har sai bayan sun dahu, ki sauke, ki tace ruwan, sannan ki kara dorawa, ki kuma hada da Tantabarun a cikin tukunyar, ki saka duk kayan kamshin da kike amfani da su, bayan ya dahu daidai misali, sai ki sauke, ki cinye duka ke kadai har da romon.
Wabillahi Taufiq.
Rubutawa: *Abu Imam (Auwal Abdullahi)*
Gabatarwa: *Abu Imam (Auwal Abdullahi)*
*- Zauren Macen Kwarai-*
*. Ga masu buqatar shiga Zauren Macen Kwarai sai a shiga ta wannan link din* 👇👇👇
https://chat.whatsapp.com/CzHKa3hRV7DDAAqmz8T1WZ