ALΖALAMI
Jama'a ina sallama,
Ni ne nan alΖalami.
Batu yau nake shirin yi,
Ga Ιalibai har malami.
Ni ne abin tsoro wurin jahili,
Kuma kayan aikin malami.
Ko'ina in har ka je galibi,
Ka ga ana amfani da ni.
Musamman ma wajen Ιalibi,
Balle Uwa Uba wajen malami.
Ban Ιauke wa kowa ba sahibi,
Hatta liman bare na'ibi.
Ko tarihi idan ka duba,
Ni ne farkon halittawa.
Kuma ni aka ba wa umurni,
Komai da komai in rubuta.
Duk abinda zai zam kasancewa,
Ni aka fara ba damar rubutawa.
Shi ya sa in ka lura da kyau,
A ke Ιauka ta da muhimmanci.
Jeka kotu inda ake hukunci,
Ko fada inda ake shugabanci.
Ni makamin Ζare dangi ne,
Mai iya shafe gari ko jahilci.
Wasu na amfani da su raba dangi,
Wasu kuma wajen yaye Ζangi.
Wasu su yi amfani da ni wajen saki,
Wasu kuma su yi wajen rubuta sadaki.
Wani lokaci a yi aiki da ni a yi cuta,
Wasu kuma su yi da ni su bada kyauta.
Ni alΖalami Ιan baiwa ne,
Don haka kowa sai ya gane.
Allah ne Ya zaΙe ni,
Na rayuwa tsawon zamani.
Jama'a da yawa na amfani da ni,
Likita, direba haΙa jami'i.
Ga shi dai arha ce da ni,
Amfani kuwa kamar magani.
Kowa na iya mallaka ta,
Ba bambanci kamar tozali.
Kai dai kawai idan ka siyan,
Ka yi aiki da ni wisely.
#haimanraees