ƘADDARAR SAFWAN 1 & 2

_*ƘADDARAR SAFWAN!*_

                   _*By*_

       _*KHADIJA I Ishaq*_

          _*(Oum Ayshat)*


DASHEN ALLAH WRITER'S ASSOCIATION 

_*JAKADIYAR DASHEN ALLAH*_
Call or WhatsApp 08162594440

***GARDAƊI*** 
Ban yarda wani/wata su juya min littafi ba ko kuma suyi amfani dashi ta hanyar da bata dace ba, ba tare da sani ba, hakan rashin adalci ne.

***JINJINA***
Jinjina gare ki Sadiya Abdullahi Umar (ohm Teemah) Queen of the writers, ina Miki fatan alkhairi akodayaushe, Muna godiya da gudummawar da kike bamu DASHEN ALLAH WRITER'S ASSOCIATION.

***GAISUWA DA FATAN ALKHAIRI*** 
Gaisuwa da fatan alkhairi gare ku ƴan uwana da abokan arziƙi, da ƙawayena, base na faɗi suna ba duka ina muku fatan alkhairi.

***SADAUKARWA***
Na sadaukar da littafi na ga dukkan masoya na, masoyan littafi na, ina muku fatar alheri cikin su harda yayana rabin raina Ibrahim, kana raina bazan manta da kai ba.

*Bis_millahir_rahmanir_rahim*


_*page*_1&2


 ________________________Kwance ya ke a kan makeken gadon shi, fari ne sosai kuma dogon saurayi kafafuwan shi sanye da takalma, gado ne na alfarma wanda kwanciya a irin wannan se wanda Naira ta zauna mu su sosai d'aki ne had'ad'd'en gaske mai girma sosai kuma ga komai na more rayuwa ya wadatu a d'akin.

Wayan shi da ke can kan drawer ne ta fara ringing tashi ya yi ya zauna, had'e da yin mi'ka, idanun shi a lumshe mi'kewa tsaye yayi domin zuwa ya d'auko wayan tafiya ya ke yana had'a hanya kai da ganin shi kasan baya hayyacin shi, lokacin da ya isa wayan ma ta yanke, wani kiran ne ya sa ke shigowa, wayan ya d'auka hannun shi na rawa da'kyar ya karanta sunan da ke rubuce a jikin BESTY SAFNA d'aukan wayan ya yi ya kara a kunne ya ce "Hello" cikin zazza'kar muryar ta ta ce "Safwan lafiya ba ka zo school ba ga shi har an kusa shiga class?", cikin canza salon murya don karta ga ne halin da yake ciki yace 

"Saf....Nahhh! ba... najin daɗi ne" maganar ya ke kai da ka ji ma kasan a buge ya ke, Daga can Safna ta ce, "Safwan 'karya za ka yi min?", "a'a ki yi..." dif..! ta kashe wayar bata ma saurari me ze ce mata ba, yayin Safwan hankalin shi ya yi matukar ta shi da fe kan shi ya yi, sannan kuma ya zube anan bacci ya kwashe shi.

AHMADU BELLO UNIVERSITY ZARIA

Can na le'ko muku abun da ke wakana d'aliban ne ke ta sintiri a cikin faffad'ar makarantar ko wa na sabgar gaban shi, wata matashiyar yarinya wanda baza ta gaza shekara sha ba'kwai ba17 na hanga kan wani dakali ita kad'ai da alama ta yi nisa ne cikin tunani fara ce sosai ga ta kyakykyawa ce sosai, kallo d'aya za ka mata kuma kasan bafulatana ce, wata ce wanda itama baza ta gaza shekarunta ba ta nufo wajen da ta ke zaune, zama ta yi tare da dafa kafad'unta tace "Safnah, me ki ke yi ke kad'ai anan ko kina jiran mutumin na ki ne", wanda aka kira da Safna ta d'ago kai tace "a'a maryam kawai ina hutawa ne kafin mu shiga class, safwan ma na kira shi yace baze zo ba", "to ai se ki ta so mu shiga class don ga sir Deniel can ma ze shiga", da sauri su ka mi'ke su ka nufi ajin don idan ya riga ka shiga baza ka shiga ba.

Yana shiga kuma kamar yanda ya saba ya fara lecture don wad'anda su ka zo late kuma se de su ka zauna a waje karatu sosai a kayi, karatun awa1 yayi musu sannan ya bada Assignment yace har wad'anda ba su zo a fad'a musu don shine a matsayinmatsayin C.A d'in su.
Bayan ya fita ne kowa yaci gaba da sabgar gaban shi wa su na karatu wasu kuma surutu, Kamal abokin Safwan ne ya ta so ya zo wajen Safnah ya ce mata "Lafiya Safwan be zo ba?", kallon shi ta yi tace "baka kira shi ba ne?", "Ehh", "to ka kira mana kaji", juya wa yayi ya koma ya zauna, ita kuwa safna tsaki ta ja don bata san me yasa bata son kamal d'in nan ba jinin su be had'u ba kwata-kwata.

Yau 'karfe sha biyu su ka ta shi makarantar Safnah na hango da 'kawar ta maryam sun jero har zuwa bakin gate d'in makarantar anan ne su ka rabu don yayan Maryam ya zo d'aukan ta kasancewar ta na Dan magaji ne, ita kuma Safnah ta na Samaru gidan su ba nisa sosai da makarantar.

Safnah tahowa ta fara yi don ta samu ko keke napep ne ta shiga zuwa gida ga garin yau rana sosai ake yi. ta dad'e sosai awajen sannan ta samu napep ta wuce gida.

Har bakin dai-dai madaidaicin gidan na su mai keken ya kaita ta ciro kud'in shi ta ba shi, ya wuce yayin da ta shiga gidan na su dauke da sallama a bakin ta, Anty na zaune a tsakar gida ta na wa Afrah kitso ta amsa cikin fara'a tare da cewa "Safnah kece da wuri haka" "Ehh anty don ma ban samu abun hawa ba da tuni na dawo", "to sannu da hanya", "sannu anty na same ku lafiya?", "lafiya lau", tace.

Sannan Safnah ta nufi d'akin ta ta ajiye jakar ta ta fito tayi alwala, kasancewar yanzu kiran sallar 'karfe d'aya 1:00 ake yi, Bayan ta yi sallar ne ta fito ta zauna gefen anty kan tabarman da ta ke zaune, anty ne ta kalle ta tace "Safnah ki zu bo abinci kici mana", "to anty" tace sannan ta nufi kicin d'in, tuwon shinkafa ne da miyar d'anyar kubewa, ya ji man shanu, zama ta yi ta fara ci, Afrah ta kalla tace "ke baki san kin girma ba baza ki de na kukan kitso ba ko", Afrah da a ka kusa gama mata kitso ai kukan ta 'kara yi don bata son magana, dai-dai lokacin sauran yaran su shigo tare da sallama sun dawo school su ma Ibrahim wanda su ke cewa khalil shine Babba se Halima, se Ummar, se Fatima, se khadija wanda su ke cewa Afrah ita ce auta, su biyar.

Zuwa su ka yi kamar yadda su saba idan sun dawo makaranta su gaishe da momin su sannan su ka ce "anty Safnah sannu da gida", "yawwa sannu" Safna ta ce musu, khalil ne yace "anty Safnah ya akayi ki ka riga mu dawowa yau", murmushi ta yi tace "ehh yau na riga ku",

Sallah su ka yi sannan Safnah ta zubo mu su abinci ta had'a wa mazan matan ma ta had'a musu sannan ta mi'ke tace "anty zan je d'aki na yi karatu" "to Safnah Allah ya taimaka", "Ameen" tace sannan ta juya ta nufi d'akin, d'akin ba lefi ya had'u don komai na masu 'karamin 'karfi an saka mata, don kawun ta na ji da ita sosai.

Uwar d'akan ta shiga ta kwanta akan gadon tare da bud'e littafin ta Assignment d'in Sir Daniel ta fara yi don tasan shi ba sau'ki, se da ta kusa gamawa da taimakon wayan ta da kuma fahimtar ta.

Aji ye littafin ta yi don wani bacci da ta fara ji kwanciya ta yi duk da tasan Lokacin Islamiyyar su ta kusa.

Baccin awa d'aya1 ta yi Afrah ta shigo tashin ta lokacin su har sun shirya ma, Bayin da ke d'akin ta fad'a ta yo alwala ta zo ta yi sallah sannan ta d'auki jakar Islamiyya ta fito, Lokacin ma su khalil sun fita su na jiran ta a waje, anty ta gani zaune a tsakar gida tana gyaran wake, tace "anty mun ta fi" "to Allah ya bada sa'a", "Ameen anty",

Fitowa ta yi ta same su a kofar gidan sannan su ka wuce, kasancewar Islamiyyar ta su a cikin anguwan su ta ke amma da d'an tafiya sosai sauri suke yi sosai don sunyi late sosai.

Wani d'an zauren gida Safnah ta shiga tare da d'aura nikaf d'in ta, don sun kusa zuwa gidan su Safwan, sannan tace su khalil su yi gaba don bata son ya tsaya bata mata lokacin.

Kamar yanda ta zata kuwa Safwan na kofar gidan su yana zaune cikin taron mutanen shi yana sanye da kayan 'kwollo ne Blue ne sunyi matu'kar yi mashi kyau sosai ko da ta iso dai-dai wajen su d'uke kai ta yi don karma ya gane ta don shi idan mutum yasa nikaf be cika gane shi, har ta wuce ta fara nisa, Safwan be ma kula ba Wani da suke kiran shi salman ya ta'bo Safwan yace "Safwan baka ga mutuniyar ta ka ba ne", kallon shi ya kai inda salman ke nuna mai, aiko ya gane ita ce mi'kewa yayi da sauri ya bita.

Safnah! Safnah!! Safnah!!!
Kamar a mafarki Safnah ta tsinci muryar Safwan na kwala mata kira, abun da ta tsana kuma yasan bata so ne shiyasa, juyowa ta yi ta hango shi can yana tahowa da gudu kallon shi ta tsaya yi har ya 'karaso nikaf d'in ta d'aga tare da kallon shi tace "to mallam makaho ya da kira haka", dariya ya yi sosai yace "se ina?" "Inda ka aike ni", dariya ya ke yi har yanzu ita kuma had'e fuska ta yi, sannan tace "ɗazu me ya naka ka shigowa makaranta", "umm!," rufe ido yayi sannan ya bud'e yace "banjin dad'i ne", "Haba Safwan ka manta nace duk abun da zaka fad'a min ka daina min 'karya" "to momi na ayi hakuri", dariya ta yi sannan tace "ai idan na haifi kamar ka bazan ganu ba tsabar tsufa ka ganni yarinya ta da ni kace min momi", "to naji", "Safwan mubar maganar wasa jiya kaje club ko?" tace, Hannu biyu ya had'a alamar neman gafara yace "kiyi hakuri wallahi kamal ya jani", "igiya ya saka ya jaka ko me, shima giyar Kamal ya d'ura maka ko?, Safwan ina so ka sani ko badan addinin mu ba don lafiyar ka ma ya kamata ka daina shan giya da sauran su Safwan ga addinin mu ma ya yi hani da hakan kai ka sani fa Safwan",
"Insha Allah zan yi 'kokarin daina wa", "yafi maka dai, to kasan yau anyi karat ai ko", "na sani har ma naje an koya min kuma na ƙara dubawa a waya", "Assignment d'in fa?" "Har na gama ma", Safnah bata yi mamaki ba don Safwan indai bangaren karatu ne baya wasa ko kad'an ko be zo ba to se ya koye shi, "to ka ga dama nayi latti ga shi ka 'kara sani na 'kara lattin ko", ta fad'a tana yin gaba, tare da cemai "se anjima", "to shikenan", ta wuce cikin sauri ta nufi makarantar.

✍️Khadeejerh Ishaq ce✍️

Comments and share pls
Post a Comment (0)