Mene ne na damuwa?
-----------------------------------------------
Ka jima kana yin addu'a, kan Allah Ya ba ka mace ta gari. Ko, ke ma kin jima kina addu'a, kan Allah Ya zaɓa miki miji nagari.
Kwatsam! Sai rana ɗaya, wanda kuke soyayya da su, suka juya muku baya. Ko; sai Allah Ya ƙaddara wani ya zo ya aure su. Ko, shi ya auri wata.
Tom! Matuƙar dama a addu'arku, da yaƙini ku ke (kun bar wa Allah zaɓi), ku kaddara, Allah Ya muku wani tanadi da ya fi na abin da ku ke so.
Abu Sa'id Alkhudry رحمه الله ya ce, Manzon Allah ﷺ na cewa:
Ba wani bawa da zai roƙi Ubangiji wata buƙata, wacce babu zunubi ko yanke zumunci a cikinta, face Allah Ya ba shi ɗayan uku:
1. A amsa masa addu'arsa (kan abin da yake so)
2. A tanada masa ladan addu'ar zuwa Alkiyama, ko
3. A canja masa da mafi alheri abin da yake roƙo, don kare shi daga wani sharri.
(Sahih At-Targheeb wa’l-Tarheeb, 1633)
Da ka kun san wannan, ba ku da damuwa, ko kwallafa rai; don wasu masoyanku da kuke tsananin ƙauna sun juya muku baya, ko sun auri wasu ba ku ba. Ba wani mutum da rashinsa cikin rayuwarka zai dakatar ma da numfashi, ko farin ciki; wannan duk a ginin tunani ne. Kar ka zauna cikin ƙunci!
A kowacce alaƙarka da mutane, akwai darussan rayuwa da in ka nutsu za ka samu, don inganta taka rayuwar ta gobe, me ya kamata ka yi, me ya kamata ka kiyaye a gaba.
✍️ Aliyu M. Ahmad
9th Rabi’ul Awwal, 1444AH
5th October, 2022CE
#AliyuMAhmad
#RayuwaDaNazari