WANE TANADI KAYI MA LAHIRARKA?

WANE TANADI KAYI MA LAHIRARKA.


"Rayuwar nan ba ta da tabbas, kana cikin tsaka da jin daÉ—in rayuwarka sai mutuwa tazo ta riskeka ko da ba tare da ta alamta maka komai ba, ka shirya ko baka shirya mata ba lokacin ka yana yi za ta zo gare ka, ka aikata mai kyau ko baka aikata ba lokacin ka yana cika za ta garzayo gareka domin ta raba ka da wannan duniyar"
-
"Kada ka taɓa tsammanin cewa kafin ka mutu dole sai mutuwa ta nuna maka wata alama ko ishara daga nan kuma za kayi ƙoƙarin tuba ko aikata kyawawan aiyuka, sannan kuma kada kace ai kai ba yanzu za ka mutu ba, sabida haka bari kawai kaci gaba da aikata abin da kaga damar aikatawa a rayuwarka"
-
"Cuta ba mutuwa bace, kamar haka ne kuma lafiya ba itace take tabbatar maka cewa ba yanzu za ka mutu ba, yo sau nawa za kaga mutum lafiyarsa ƙalau, da kansa ma ya ɗauki jiki ya fita yawon sa ko neman abincinsa, amma sai dawo dashi gida akayi a mace. Sau nawa kuma za kaga mutum a kwance a asibiti kowa ya ɗebe masa tsammanin rayuwa, amma kuma sai kaga ya miƙe yaci gaba da rayuwarsa, to ka ɗauki izna daga mutuwa, haƙiƙa abu ne mai sauƙi kaga ta ɗauke wanda yafi kowa lafiya a layinku, ta bar kuma wanda yafi kowa tsananin cuta yaci gaba da rayuwarsa"
Post a Comment (0)