𝐙𝐀𝐌𝐀𝐍 𝐆𝐈𝐃𝐀𝐍 𝐆𝐀𝐃𝐎
Haɗaka tsakanin mahaifa da matan 'ƴaƴansu takan haddasa mutuwar aure a ƙasar Hausa. In mutum yana gidan gado za su iya haɗa banɗaki da mashiga shi da mahaifinsa da matarsa, wanda hakan yana jawo takura.
A lokuta da yawa mahaifi zai iya kai kukan matar ɗansa ba ta gaishe shi ko kuma ba ta girmama shi in sun yi 𝑘𝑖𝑙𝑖𝑦𝑎
Akwai wanda na sani, mahaifiyarsa ce ta sakar masa matarsa bayan ya yi tafiya, saboda illar zaman gidan gado 😳.
Wani abokin aikina ya ba ni labarin cewa; ƴar ɗansa tana aure a wani gida, sai mijinta yazo yana dukan ta, sai uban mijin yazo ya sanya hannu aka ci gaba da dukanta tare da shi 😳. In dai ba a gidan gado ba, babu inda zaka samu wannan kwamacalar.
Wani suruki ya ga matar ɗansa tana abin da ba daidai ba, ya kwaɓe ta, sai ta kada-baki tace masa: "ka ƙyale ni tunda ba kai ne ka auro ni ba", shi kuma yayi amfani da damarsa yace da mijin ya sake ta, an yi ta zuwa biko amma ya cije yace ko da ya tafi Lahira, to in an dawo da ita bai yafe ba.
Akwai uwar mijin da in matar ɗanta tayi kwalliya, itama sai taci kwalliya, ta harɗe ƙafa ta zauna a tsakiyar gidan gado saboda tsabar kishi, da yake matar ɗan nata ƴar duniya ce, sai tace: "in kin isa ki je ki kwana tare da shi" 🙆🏻♂️.
Irin wannan rainin ba'a samun sa sai a gidan gado ko haɗaka.
Duk mutumin da bai takura ba, to kar yayi aure ya zauna a gidan gado.
____
𝑫𝒂𝒈𝒂 𝒍𝒊𝒕𝒕𝒂𝒇𝒊𝒏 '𝑴𝒂𝒏𝒚𝒂𝒏 𝑴𝒂𝒕𝒔𝒂𝒍𝒐𝒍𝒊𝒏 𝑨𝒖𝒓𝒆....', 𝒏𝒂 𝑫𝒓. 𝑱𝒂𝒎𝒊𝒍𝒖 𝒀𝒖𝒔𝒖𝒇 𝒁𝒂𝒓𝒆𝒘𝒂.