*HANYOYIN CIN NASARA A RAYUWA*
```// 12```
.
.
KARATU FA DOLE NE
Ko ni nakan fadi haka, amma kuma wanne? Karatun addini ko na boko? Ga wanda ya san akwai bambanci kenan, ni a iya sanina ba ilimin da addini bai zo da shi ba sai dai in ba shi da mahimmanci ko amfani ga dan adam, ilimin rayuwannan da kake gani shi ne mafi mahimmanci a wurin kowa don haka dole ka yi shi in kana son cin nasara a rayuwarka, za ka taras wani ya yi Furamare ne ya tsaya, tsakani da Allah ba za ka hada shi da wanda bai taba taka makaranta ba, wani ya yi Sakandare ne ya ce "Nan zan tsaya".
.
To irin wannan da ya tsaya a Sakandare ba za ka taba tunani a zuciyarka zai iya zama malamin jami'a ba, ko malamin Sakandaren da ya yi ba zai zama ba sai in ya dawo ya ci gaba da karatu zuwa gaba da Sakandaren, haka mutumin da a rayuwarsa matuqin mota ne da ya koya a tasha ya iya, ya kwashe kimanin shekara 25 yana tuqi rana daya ba zai ce kai na gaji yanzu jirgin sama zan koma tuqi ba, iliminsa bai kai nan ba, komai gwanancewar mutum a tuqin keke rana guda ba zai hau babur ya tuqa ba sai in ya koyi yadda ake yi a karance ko a aikace.
.
Kamar bakanike ne, don mutum ya yi shekaru yana gyaran keke ba zai ce yau na koma gyaran mota don dukansu biyu hawansu ake yi ba, kamar yadda ka san ni da kai shekarummu guda ni ina da mata 2 kai ba ka taba aure ba ba za ka ce masaniyarmu da mace guda ne ba, shi karatu komai kasawarsa dole sai an yi shi, in ba ka taba aure ba tashi guda aka ba ka mata biyu, ni kuwa na taba zama da su a lokaci guda matsalar rayuwa ta sa na rabu da daya ko dukansu biyu dole yadda zan tafiyar da sabbin matan ya bambanta da yadda za ka yi, ba komai ne ba sai karatun da na yi a baya, sau da yawa kallon baya kan taimaka wa mutum ya san yadda zai tafiyar da gaba.
.
Amma fa gaba daban baya daban, mai son cin nasara a rayuwarsa kar ya taba raina ilimi don koya yake, a lokacin da mutum ya yi Furamare ya ce daganan na gaji kenan abokan karatunsa za su wuce gaba, Qur'ani kuma ya tambayemu a sifar qalu-bale ya ce: "Shin masana da marasa sani za su yi daidai?!" Ya ce "Ko a kwatance ba daidai suke ba" duk wanda ya wuce ka har abada ya sha gabanka, sai dai ka fi shi a wani abin ko ka dawo ka shiga gabansa, yadda ka san jahilan masu kudi ba su sha'awar su zama talakawan masu ilimi, haka talakan malami bai da burin zama jahilin mai kudi.
.
Kowa buri yake ya hada biyu, ga kudi ga ilimi, hakan kuma ba zai hadu ba sai da karatu, duk dan kasuwan da yake da ilimi ya fi sanin yadda zai bunqasa kasuwancinsa, to bare babban ma'aikaci, gwamnati kanta takan qimanta mutum ne da yanayin matakin karatun da ya taka, ba cewa muke kowa sai ya yi zurfi a karatun boko ba, amma iya karatun mutum iya inda zai tsaya, wanda ya tsaya a facin keke bai yalwata tunaninsa zuwa na babura da manyan motoci ba tabbas zai mutu a facin keke, domin iyakarsa kenan.
.
Wanda yake ganin yana da kayan facin keken qila yana buqatar inji ne kawai da manyan sifanonin da za su taimake shi wurin kwance tayar mashin, sai ya fara tara kudin inji, ya sayi kayan aiki tabbas wata rana za ka ji ya fara facin babur, qila kuma ya bar wa yaransa facin keke, daganan zai fara saka wa mota iska ana biyansa masu motoci su fara zuwa a tsammaninsu har faci yana yi, daganan zai fara tunanin to me zai hana ya fara facin ma? Qila ya fara tattauna wasu batutuwa da masu facin mota din, wata rana sai dai ka ji ya fara sayo kayan aiki, kamin ka ankara sai dai ka ga motoci har ya fara facin tayoyinsu, ya fadada tunaninsa kenan.
.
Duk abinda mutum yake sha'awa a rayuwa ya yi karatu kawai, kar ya damu da abinda yake karantawa idan ya saki layi tun farko, ya fara tunanin yadda zai kai ga burinsa kawai matuqar yana tunanin cewa rayuwarsa ba za ta yi masa dadi ba sai da cikan burinsa, na san wani babban dan jarida wanda kimiyar noma kawai ya karanta sai ga shi ya sami kansa a fagen jaridar da ya jima yana haqilo, na san wanda addinin muslunci ya karanta, ba harshe ba bare a ce suna kusa, shi ma dai ya zama babba a harkar jarida yana gogayya da manyan 'yan jaridu a yau, na kuma san wanda ya karanta aikin likita kuma yana da buri game da harkokin addini, shi ma yau daya ne daga cikin manyan mutanen da ake alfahari da su a duniya ta fannin ilimin addinin.
.
Duk wadannan sun cimma burinsu ne ta wajen karatu koda kuwa abinda suke nema bai yi daidai da karatun da suka yi ba, sai dai kuma karatun ya ba da gudummuwa gwaggwaba wurin cimma burinsu na samun abinda suke so a rayuwa, shi karatu ko ba ka riqe biro ba, ba ka zauna a aji ba sunansa karatu, ba kuma za a taba hada ka da wanda bai yi ba har abada, kusan kowa ya san haka, shi ya sa in mutum ya yi kwaba za ka ji ana cewa "Ka ji, wai Dr kenan!" Duk kuwa da sanin cewa kwabar da ya yi ba a fanninsa ba ne, ma'ana karatun da ya yi bai taimaka masa da komai ba a wannan wurin.
Rubutawa:- Baban Manar Alqasim
Gabatarwa:- Yusuf ja'afar Kura
Daga
*MIFTAHUL ILMI*
```Ga masu sha'awar Shiga Zauren MIFTAHUL ILMI WhatsApp sai a aiko da cikakken suna ta WhatsApp zuwa ga lambar Mu 07036073248```