WASU MATAN // 10
Wani lokacin mace na mugun qaunar namiji, amma yanayin mu'amallarta da shi sai ya lalubi qaunar sama da qasa ya rasa, a qarshe ya yanke wata muguwar shawarar da ba za ta yi wa kowa dadi ba, haka ya faru da wannan matar.
.
Maigidanta dan jarida ne, kuma yana jin dadin aikinsa, don suna samun abin rufin asiri, wani lokaci abin ya zo da yawa kuma a kashe su a gidan, ranar da babu kuma akan dan sha wahala, wata rana haka kurum shaidan ya zuga ta, ko wahayin shedan ne oho, ta bude wuta kan cewa dole sai ya canja halinsa, tana ma ganin dole ya rabu da aikinsa tunda sukan sami kansu cikin wani hali a wasu lokutan, shi kuma ya kafe kan cewa ba abinda zai yi.
.
A qarshe ta koma gidansu, shi kuma ya qi zuwa biko, aka dauki tsawon lokaci, bai je ba, ta fara matsa masa lambar sai ya sake ta, ya rufe ido ya ba ta takarda, haka ta sa qafa ta tsallake 'ya'yanta 4, daya namiji da qanninsa mata guda 3, ubansu ya jure wannan jarabawar ya ci gaba da zama da yaran, komai shi yake musu, ana cikin haka sai wata dalibarsa da ta san abinda yake faruwa ta fara magana da shi, har tana kawo masa abinci, ta fara kula da yaransa kamar ita ta haife su, har dai qaunar da take buqata ta qullu tsakaninsa da ita.
.
Nan ne fa matarsa ta farko da ya sake ta ta fara haukar cewa sam ba ta yarda ba, ta lashi takobin ba wata mahalukiyar da za ta shiga dakinta, ta bi duk hanyoyin da za ta hana faruwar abin, da dai ta ga cewa ta kasa isa inda take so sai ta ja kunnensa da cewa za ta iya kashe kanta matuqar ya ce zai auro wata ba ita ba.
.
Lura da irin wahalar da ya sha a hannunta, sai ya yi watsi da ita, jama'a sun ji masa dadi da ya rabu da ita, don ya dawo hayacinsa, dama baqi ne har launinsa ya canja ya zama fari, alamar ba ya jin dadi, kenan rabuwa da ita shi ya fi.
.
Aka sa ranar daura aure, ranar na zuwa aka daura auren, sai dai abin da zai ba ka mamaki tun ranar har maganannan tamu ba wanda ya sake saka ta a ido, ba wanda ya san inda ta je ko halin da take ciki, na ce irin wadannan matan in dai qaunar ta kai haka me zai sa ba za su haqura su zauna da masu gidansu tun farko cikin rufin asiri ba?
Rubutawa:- Babban Manar Alqasim
Gabatarwa:- Yusuf Ja'afar Kura
Daga
*MIFTAHUL ILMI*
ZaKu iya Bibiyar Mu a
Facebook⇨https://www.facebook.com/pg/Miftahulilmi.ml
Telegram⇨https://t.me/miftahul_ilmi
WhatsApp⇨ https://wa.me/2347036073248