Wasu Maza 4 Da Basu Dace Mata Su Kula Su Ba

Wasu Maza 4 Da Basu Dace Mata Su Kula Su Ba:







Ba duk namiji bane ya dace da kulawarki ba. Duk namiji bane zaki bashi zuciyar ki ba. Ba duk namiji bane zaki amince masa da ya aureki ba duk zakuwarki da kina son aure.

Akwai wasu jerin maza guda 4 da duk son aureki idan kika sake kika aure su sai kin gwammace da kin yi zama baki da aure. Wadannan mazan sune:

1: Namji Mara Ibada: shi rashin ibada ya kan iya mutum ya zama baida da duk wani imani ko tausayin da ake bukata magidanci ya kasance da su ba. Muddin kika fahimci irin wannan namijin na sonki to kada ki kula shi.

2: Namiji Mai ÆŠagawa: Kada ki sake ki kula namijin da yake da dagawa, ji da kai takama da gadara, muddin kuwa kika bashi dama ko da na rana daya ne sai ya nuna miki iyakar ki.

Sune mazan da suke iya duban cikin idanuwan mace su goran ta mata su kuma kaskantar da iyayena.
Sune mazan da suke ganin auren mace tamkar alfarma suka mata da suka aure ta.

3: Namijin Da Bai Ganin Darajar Mata: Awaki mazan da suke ganin ita mace ba abakin komai take ba. Irin su basu ganin darajar mace suna iya mata wulakanci a duk inda ya kama kuma ko a gaban wa.

Irinsu suna ganin mace kawai abar jima'i ce aji dadi da ita daga nan bata da wani amfani sai kuma lokacin da wannan bukatar ta taso.
Muddin kika baiwa irin wadannan mazan damar a zuciyar ki zaki gwammace kida da karatu.

4: Maza Makaryata: duk inda ka samu makaryaci zaka kuma sameshi ya goyo yaudara a bayan sa. Don haka makarya maza suna da hadari da mace zata basu amincewarta saboda rashin sanin tabbacinsu.
Yadda yake shinfida miki zance haka nan yake shinfidawa wata acan. Don haka mu'amala dashi yana tattare da matukar hadari.
Post a Comment (0)