ABUBUWA GUDA TAKWAS SUNA JANYO ALBARKA A GIDA

ABUBUWA GUDA TAKWAS SUNA JANYO ALBARKA A GIDA

Samun albarka acikin gida yana nufin samu Walwala da kwanciyar hankali da yalwar arziki da yawan ibada mai yawa da karanci sabon Allah da samu zuri'a ta kwarai. Allah Madaukakin Sarki da Annabi s.a.w sun bamu labarin wadansu abubuwa da idan muka aikatasu agidajenmu zamu sami albarka masu yawa a gidanmu._

1-YAWAITA KARATUN ALQURANI MAI GIRMA

Allah yana cewa:_
(وهذا كتاب أنزلناه مبارك)

Ma'ana: (Wannan wani littafine da muka saukar dashi mai albarka).

Wato Allah ya sanya alqurani mai albarkane ta kowace bargane albarka wajan karanta shi da wajan sanin ma'anonisa da wajan jin tilawarsa.

Babu wani abu da yake janyo albarka agida kamar yawaita karatun alqurani acikinsa, Annabi s.a.w yana kwadaitar da mu yawaita karatun alqurani a gida gaba daya sannan ya kara kwadaiyar damu karanta wasu surori dan samu albarka da falala da kariya daga aljannu da shaidhanu a gidajen mu Kamar:-

Suratul Baqra Gaba daya.

Suratut Tabara.

Suratul Ãli Imran.

Qulhuwa da Falaqi da Nasi da dai sauransu.

2-AMBATON ALLAH LOKACIN SHIGA GIDA DA LOKACIN FITA DA FADAR BISMILLAH LOKACIN CIN ABINCI:

Annabi s.a.w yana cewa: (Idan mutum yazo shiga gidansa sai ya ambaci Allah Madaukakin Sarki a lokacin shiga gidansa da lokacin cin abincinsa, sai Shaidhan yacewa sauran Shaidhanu baku da wajan zama agidan nan kuma baku da abinci acikinsa)._

```ZIKIRIN SHIGA GIDA```

Na farko:

(السلام عليكم و رحمة الله و بركاته
_"ASSALAMU ALAIKUM WA RAHMATULLAHI WA BARAKATUHU".
 
_lSaboda fadin Annabi s.a.w: (Mutane guda ukku dukkansu hakkine akan Allah idan suka rayu, Allah ya azurtasu kuma kuma ya isar masu,idan kuma suka rasu ya sanya su a Aljanna. Wanda ya shiga gidansa yayi Sallama. Wannan yana cikin lamuncewar Allah wanda ya fita zuwa Masallaci, shima yana cikin lamuncewar Allah. Wanda ya fita zuwa wajan daukaka kalmar Allah, Yana cikin lamuncewar Allah.
@صحيح الترغيب 321 الألباني

Na biyu:
(بسم الله)
"Bismillahi"

Saboda fadin Annabi s.a.w: (Idan mutum yazo shiga gidansa sai ya ambaci Allah Madaukakin Sarki a lokacin shiga gidansa da lokacin cin abincinsa, sai Shaidhan yacewa sauran Shaidhanu baku da wajan zama agidan nan kuma baku da abinci acikinsa).
@مسلم، برقم ٢٠١٨

Na Uku:
(بِسْمِ اللـهِ وَلَـجْنَا، وبِسْمِ اللَّهِ خَرَجْنَا، وعَلَى اللَّهِ رَبِّنا تَوَكَّلْنَـا، ثُمَّ لِيُسَلِّمْ عَلَى أهْلِهِ))
"BISMILLAHI WALAJNA, WABISMILLAHI KHARAJNA WA'ALA RABBINA TAWAKKALNA" Sannan sai yayi Sallama).
@أخرجه أبو داود (325/4) [برقم (5096)]، وحسن إسناده العلامة ابن باز في ((تحفة الأخيار)) (ص 28).

```ZIKIRIN FITA DAGA GIDA```

Na farko:
(بسم الله، توكلت على الله، لا حول ولا قوة إلا بالله)
"BISMILLAHI TAWAKKALTU ALALLAH WALAHAULA WALA QUWWATA ILLA BILLAHI".

Saboda fadin Annabi s.a.w Ga wanda yayi wannan zikiri lokacin fita daga gida, Sai Yace da shi an isar maka, Kuma an baka kariya, kuma an shiryar dakai, kuma an tseratar da kai daga shaidhan. Sai Shaidhan ya fadawa wani daga cikin Shaidhanu yayi zaka iya da mutumnin da aka bashi kariya aka shiryar da shi aka isar masa?).

@الكلم الطيب 59 الألباني

Na Biyu:

(بسمِ اللهِ ، توكَّلْتُ على اللهِ ، اللهم إِنَّا نعوذُ بكَ مِنْ أن نزِلَّ ، أوْ نَضِلَّ أوْ نظلِمَ أو نُظْلَمَ ، أو نجهلَ أو يُجْهَلَ علينا)

"BISMILLAHI TAWAKKALTU ALALLAH ALLAHUMMA INNA NA UZUBIKA MIN AN AZALLA,AU NADHILLA AU NAZLIMA AU NUZLIMA AU NAJHALA AU YUJHALA ALAIYA"

Saboda Hadisin da yake cewa Annabi s.a.w ya kasance idan zai fita daga gida yana fadar wannan zikiri).
@صحيح الجامع 4708 الألباني

Allah Ne Mafi Sani

```Mu Hadu a Darasi Na Gaba Insha Allah```

Post a Comment (0)