TSOTSON FARJIN MACE YAYIN SADUWA!!!
Tambaya
Assalamu alaikum, M. Na kasance ina tsotsan azzakarin mijina, shi kuma yana wasa da gabana da harshensa kafin mu sadu, ina matsayin haka a addinin musulunci.
Amsa
To 'yar'uwa hakan ya halatta, ba matsala a sharian ce, saboda an rawaito halaccin haka, daga magabata, daga cikinsu akwai Imamu Malik, saidai ya wajaba a tabbatar an tsaftace wurin musamman farjin mata, saboda a bude yake, sannan kuma wuri ne da ake yin haila, ake kuma zuba maniyyi, ga shi kuma yana kusa da wajan yin bahaya, wasu masana likitanci suna bada shawarar cewa : a dinga wanke wurin da gishiri kafin a tsotsa, saboda neman kariya.
Allah madaukakin sarki a cikin suratul Bakara aya ta: 223, ya kwatanta mace ga mijinta da gona, wannan sai ya nuna dukkan bangarorin jikinta ya halatta a ji dadi da su, in ban da cikin dubura wacce nassi ya togace.
Allah ne mafi sani.
Duba : Mawahibul-jalil sharhin Muktasarul Khalil 3\406
BANBANCI TSAKANIN...
👉MANIYYI
👉MAZIYYI
👉WADIYYI
Dan Allah kudinga yin share dinsa domin ku sami ladan wadansu su amfana.
Babu jin kunya a cikin sanin addini!
Nana A'isha (R.T.A)tana cewa:
"Allah ya jikan MATAN MADINA kokadan KUNYA bai taba hanasu neman sanin addininsu ba"
Dan haka ga banbancin dake tsakanin su kamar haka:
(1a). MANIYYI
Maniyyin namiji: ruwane mai kauri FARI wanda yake fitowa yayin babbar sha'awa kamar saduwa, ko wasa da zakari.
Sannan yana tunkudo juna lokacin dayake fitowa, kuma warinsa yana kama da warin hudar dabino, ko damammen gari, Idan ya bushe yana kamshin kwai.
(1b). MANIYYIN MACE:
Ruwane TSINKAKKE, MAI FATSI-FATSI,
Wani lokacin kuma yana zuwa FARI, wanda yake fitowa yayin babbar sha'awa kamar saduwa, ko wasa da farji.
Sannan yana tunkudo juna lokacin da yake fitowa, zataji tsananin sha'awa da dadi lokacin daya fito.
Kuma warinsa yana kama da warin hudar dabino ko damammen gari, Idan ya bushe shima yana kamshin kwai.
Sannan sha'awarta zata yanke bayan fitowarsa.
HUKUNCIN FITAR MANIYYI shine:
YANA WAJABTA WANKA.
(2). MAZIYYI:
Ruwane tsinkakke da yake fitowa, yayin karamar sha'awa, kamar tunanin aure ko kuma tuna wacce kakeso, ko matarka, ko kallon matar ko namijin da kike sha'awa.
Haka kuma yana fitowa yayin wasa tsakanin miji da mata, saidai shi baya tafiyarda sha'awa, kuma wani lokacin ba'a sanin yafito.
Malamai suna cewa:
Maziyyi yafi fitowa mata, fiye da maza.
HUKUNCINSA SHINE A WANKE FARJI GABA DAYA, DA KUMA INDA YA SHAFA, KUMA A SAKE ALWALA.
(3). WADIYYI
Wani ruwane mai KAURI dayake fitowa a karshen fitsari, ko kuma karshen bahaya ga wanda ya jima bai yiba, yana fitowa ga wadanda ba suda aure, ko wadanda suka yi nisa da abokin rayuwarsu ta aure, ina nufin namiji ko mace.
YANA DAUKAR HUKUNCE-HUKUNCEN FITSARI.
Ya Allah kakaramana Imani da fahimta.Gaskiya ”Allah ka bamu ikon fadar gaskiya komai zafinta ko dadin ta.
Allah shine mafi sani!!!