FITINTINU SUN MANA YAWA, GA KUMA FIRGICI, MENENE MAFITA?

FITINTINU SUN MANA YAWA, GA KUMA FIRGICI, MENENE MAFITA?

Tambaya :

Assalamu Alaykum Akaramakallah, da fatan rubutuna zai zo maka cikin koshin lafiya. In cikin matsala da jarabawa kusan shekara biyu yanzu. Na farko, na dauko wata yarinya na riko, ta gamu da aljanu, ta koma gida, da zata dawo, ta dawo da jan kaya wai ta sa ajikinta duk ranar lahadi, wai ta samu sauki. Maigida na ya hanata sa kayan. Bayan kamar wata biyu, muka fita kasuwa, dukammu muka fita kasuwa sayayya, maigida na ya ga pilowa ya saya, bayan hakan muka fara ganin gashin tsuntsaye a gida. duk lokacin da karenmu yayi kuka sosai, tabbas zamu kwashe gashin da yawa a gida ranar. Muka shiga addu'a da karanta alquran cikin gida. Yarana uku duk yammata, duk safiyan Allah za su tashi da idanunsu jawur, da maigidana. Ni kuma, ina cikin yin azkar dare da rana, abunda suka sa min shine firgita da tsoro, a duk lokacin da karenmu ya fara kuka ko da rana ko da dare, sai in kama firgita sosai da kuma ganin wadanan gashin. Mu na nan da haka, Allah ya nuna mamu pilowan nan da muka saya gashi ne cike da ita. Muka kone ta. Bayan haka ne damuwan ya karu. Gashinne cikin kayan sawanmu, da na yara, karkashin gadonmu da na yara na, akan gado, cikin mota ne ko ina agida attah net na windodin mu, har ata abincinmu. Muka bar gidan, inda muka koma, suka biyo mu, kuma duk lokacin da muka shiga kauyenmu, sai su biyo mu gidan kauye. Ayanzu dai haka, muna sabon gida, kuma sunanan da mu, akan kujerunmu, cikin net na windodin gida ne, gashin na nan. Yanzu ma ciki gareni na wata shidda. Duk magungunan da zikirkiri na sunnah, muna tayi, yarinya mai aljanin kuma har yanzu suna nan da ita, sun sha yin alkawari zasu fita amma ba su fitaba, yanmata ne musulmai ajikinta. Ba kuma wanda zai iya gaya mana ga abunda ke damumu. Mun sha magunguna da na wanka, da hayakin mun gaji. Yanzu dai har, na bar duk magungun, amma ban bar yin addu'a ba. Akaramakallah, ko za'a iya taimaka min da addu'a ko shawaran bi na samu maganin abubawan da Ikon Allah anan. Allah ya saka da alkhairi..

Amsa:

Wa alaikum assalam To 'yar'uwa tabbas ba a warware sihiri ta hanyar sihiri, saidai ana iya warware sihiri ta hanyar ayoyin Alqur'ani, wasu malaman sun yi bayani cewa : ana iya warware sihiri ta hanyar karanta Ayatul-kursiyyu da Kuliya da Iklas da Falaki da Nasi, da kuma aya ta : 117 zuwa ta 122, na suratul A'araf, sai kuma aya ta : 79-81 a suratu Yunus, sannan sai a hada da aya ta : 65-70 a suratu Dhaha, za'a karanta su, sai a tofa a ruwan da aka zuba magarya guda bakwai.
Sannan ina yi miki wasici da yawan karatun suratul Bakara,saboda muhimmancinta wajan kore shaidanu, kamar yadda ya tabbata a hadisi, kada ki manta da karanta addu'o'in shiga bandaki da na bacci, da azkar na safe da yamma, da kuma tuba daga zunubai, saboda wasu musifun zunubai su ke kawo su.
Idan fitintinun suka cigaba za ku iya mayar da 'yar rikon, saboda zai iya yiwuwa a tare da ita shu'umcin yake, tun da a baya ba ku ga haka ba, yana daga cikin ka'idojin sharia, ana tunkude cutar da ta shafi mutane da yawa ta hanyar kau da kai akan cutar da za ta shafi mutum daya, wannan ya sa mayar da ita bai zai zama laifi ba.
Yana daga cikin hanyoyin tunkude fititinu, nisantar dukiyar haram, in har a kayan gidan da kuke ciki akwai dukiyar da kuka mallaka ta hanyar haram ya wajaba a fitar da ita zuwa mai ita.                         
                                                                                                Yin sadaka da taimakawa musulmi yana warware mushkiloli, saboda duk wanda ya yayewa wani bakin ciki, Allah zai duba dumuwarsa, hakura da wancan shaidanin karen na ku yana da muhimmanci, saboda mala'iku ba sa shiga cikin gidan da yake akwai kare, kamar yadda ya tabbata a hadisin Bukhari.                                                      In har kin bi wadannan shawarwari ina ga za ki samu nasara mai girma.
Allah ne mafi sani

Amsawa

DR JAMILU YUSUF ZAREWA
7\2\2016.

Post a Comment (0)