YA YI WA MATARSA ZIHARI SAI YA SAKE TA KAFIN YA YI KAFFARA?

YA YI WA MATARSA ZIHARI SAI YA SAKE TA KAFIN YA YI KAFFARA?

Tambaya:

Assalamu Alaikum, Malam ina da tambaya? Namiji ne ya yi wa matarsa zihari, maimakon ya yi kaffara sai ya sake ta, ya sake wani auren. Malam ya matsayin wannan sakin da matsayin auren?.

Allah ya bada ikon isar da wannan sako ga  Malam.

Amsa:

Wa alaikum assalam, Auransa na biyun ya inganta saboda ba su da alaka da juna.

Wasu Malaman sun tafi akan cewa mutukar saki uku ne, to wancan ziharin ya warware, amma in saki daya ne kuma ya yi kome, to bai halatta ya taba ta har sai ya yi kaffarar ziharin, kamar yadda Ibnu Khudaamah ya fada a cikin Al-Mugni.

Allah ne mafi sani.

Amsawa:

Dr Jamilu Yusuf Zarewa
01/06/2017.

Daga: ZAUREN FIQHUS SUNNAH

Post a Comment (0)