HUKUNCIN KALLON WASAN KWAIKWAYON ANNABAWA
Tambaya
Assalamu Alaikum
Malam Don Allah Tambaya Na ke da shi Da Fatan Za'a Fahimtar da ni. -wai Shin Kaset din da akeyi na Tarihin Annabawa Ya Halatta A Kalle shi ? Allah Ya Saka Da Alkhairi.
Amsa
Wa'alaykumussalam, To dan'uwa malamai da yawa sun haramta yin wasan kwaikwayon annabawa saboda dalilai kamar haka:
1. Hakan zai iya bude kofar da wasu masu kallon za su yi isgilanci ko ba'a ga annabawan Allah, isgilanci ga annabawa kuma yana iya fitar da mutum daga musulunci, kamar yadda aya ta: 65 a suratu Atttauba ta yi nuni zuwa hakan.
2. Wasu daga cikin masu shirya film din suna wuce gona-da-iri, kamar masu nuna annabi Isa a matsayin Allah, addinin musulunci kuma ya haramta duk abin da zai kai a riki wani annabi ko managarci a matsayin Allah.
3. Irin wadannan wasannin na kwaikwayo, suna ragewa annabawa matsayi, saboda masu film din suna cakuduwa da matan da ba muharramansu ba, wanda hakan kuma ragewa annabawa kima ne.
4. Kasancewar hakan ya sabawa hikimar Allah ta sanya shaidanu ba sa iya kama da Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, kamar yadda ya zo a hadisi.
5. Kasancewar hakan zai jawo aki girmama annabawa, a kuma yi musu karya, domin wasu masu yin wadannan fina-finan mutanen banza ne, ka ga sai a dinga kallon annabawan da siffar wadannan.
Allah ne mafi sani.
13/6/2014
Amsawa:-Dr. Jamilu Zarewa.
Gabatarwa:- Ãbûbäkår Êkâ.
Ya kai dan uwa mai Albarka ka taya mu yada wannan karatu/sako zaka samu lada mai yawa, domin yada ilimi yana da daga cikin Abubuwan da suke kusan ta bawa ga Mahalicci.
_____________________________________
» Zauren MIFTAHUL ILMI📖 (WhatsApp).
→ Ga ma su sha'awar shiga Zauren MIFTAHUL ILMI a whatsApp sai a turo da CIKAKKEN SUNA zuwa ga lambar mu
(07036073248) ta whatsApp
Allah ya saka da Alkhairi
ReplyDelete