HUKUNCI KAYYADE HAIHUWA (FAMILY PLANNING)

HUKUNCI KAYYADE HAIHUWA (FAMILY PLANNING)

                           Tambaya:

Shin ko akwai dalilai na shariah da suke halatta mace ta juyar da mahaifarta ko kuma ta samu tazarar haihuwa?

                               Amsa:

To dan uwa amfani da abin da zai kayyade iyali, ya kasu kashi biyu
1. Ya zama zai hana daukar cikin kwata-kwata, a nan bai halatta ba, saboda ya sabawa manufar shari'a na yawaita al’uma, kuma 'ya'yan da take da su za su iya mutuwa sai ta koma mai wabi.

2. Ya zama an tsayar da shi ne na dan wani lokaci, kamar mace ta zama tana yawan haihuwa kuma cikin yana wahalar da ita, sai ta yi nufin ta tsara haihuwarta ta yadda za ta haihu duk bayan shekara biyu ko makamancin haka, to wannan ya halatta in dai miji ya bada izini kuma ba zai cutar da matar ba, dalili akan haka shi ne sahabbai sun kasance suna azalu a zamanin Annabi S.A.W don kar matansu su dauki ciki, kuma ba'a hana su ba, kamar yadda Bukari ya rawaito daga hadisin Jabir mai lamba ta: 4911.

Abin da ake nufi da azalu shi ne idan namiji yana saduwa da matarsa idan ya ji maniyyi zai fito sai ya fitar da azzakarinsa ya zubar da maniyyin a wajen farji.

Duba Dima'uddabi'iyya na Ibnu Uthaimin shafi na 57.

13/7/2014

Amsawa:- Dr. Jamilu Zarewa.
Gabatarwa:- Ãbûbäkår Êkâ.

DAGA ZAUREN

DOMIN SHIGA WANNAN GROUP  08029399000 ko 08143979048

Post a Comment (0)