MA'AIKACIN GWAMNATI, BA ZAI AMSHI KYAUTA BA !!!
Tambaya
AsSalamun alaikum malam, malam ina da tambaya ne?. Ni ma'aikacin gwamnati ne a wata hukuma ta gwamnatin taraiya, sai aka tura ni na dinga kula da wani aiki da aka bawa wani kamfani shima kuma kamfanin ya bawa wani kamfanin da ya taimaka masa da aikin, amma malam na tsaya da gaske wajen kula da aikin anyi yanda ya kamata, bayan an gama sai suka bani kudi wanda ni ban tambaya ba.malam menene yanayin wannan kudi a musulunci?.
Amsa
Wa alaikum assalam,
A zahiri wannan kudin da ka amsa Haramun ne kuma cin hanci ne, saboda an baka ne saboda kujerarka, inda a gidanku kake da ba zasu baka ba.
Annabi S.A.W. yana cewa a cikin hadisin da Abu-dawud ya rawaito "Duk wanda muka ba shi aiki sannan muka sanya masa albashi akan aikin, to duk abin da ya karba bayan haka cin-hanci ne"
Annabi S.A.W. ya fusata sosai kuma ya yi maganganu masu zafi lokacin da ya aika IBNU-ALLUTBIYYA karbo zakka amma kuma sai aka ba shi kyauta ya karbe kamar yadda Bukhari da Muslim suka rawaito.
Hadisan da suka gabata suna nuna cewa: Haramun ne ma'aikacin da yake da albashi ya amshi kyautar da aka yi masa saboda aikinsa, in har ya amsa kuma to ya ci wuta bal-bal.
Idan ma'akaicin gwamnati yana karbar kyauta ta hanyar kujerarsa: almundahana da suturta aibi da yin alfarma ga wadanda ba su cancanta ba za su yawaita a bayan kasa, wannan yasa musulunci ya haramta hakan.
Idan aka bawa ma'aikacin gwamnati kyauta domin Allah ko kuma soyayya ba don kujerarsa ba, ya hallata ya amsa, saboda Annabi S.A.W. yana karbar kyauta har ma ya yi sakayya akanta.
Allah ne mafi sani.
Dr, Jamilu Zarewa
16/11/2017