MACE ZATA IYA YIN AUREN KASHE WUTA?

MACE, ZA TA IYA YIN AURAN KASHE WUTA ! !

03 -02 -1439
23 -10 -2017

           Tambaya

Assalamu Alaikum
MALAM menene hukuncin wadanda sukayi auran kisan wuta suka maida aurensu, kuma menene hukuncin auren nasu?

              
                Amsa

Wa alaikumus salam

Auran kisan wuta bai halatta ba. Saboda Annabi (S.a.w) ya la’anci wanda ya yi da kuma wanda aka yi saboda shi, kamar yadda Tirmizy ya rawaito kuma ya inganta shi Idan miji ya yi aure da niyyar halattawa mijin baya, auran batacce ne, amma idan mace ce ta yı da wannan niyyar, kuma mijin da ta aura bai sani ba, to auran yayi.

Saboda ba dole ba ne mijin ya sake ta. Yana daga cikin Ka’idojin sharia:
ﻣﻦ ﻻ ﻓﺮﻗﺔ ﺑﻴﺪﻩ ﻻ ﺃﺛﺮ
ﻓﻲ ﻧﻴﺘﻪ
Duk wanda babu saki a hannunsa, to niyyarsa ba ta da tasiri.

Allah shine mafi sani 

Amsawa:
Dr. Jamilu Yusif Zarewa
Abibiyemu a shafin facebooks
www.facebook.com/Islamicsunnah

*
Kota WhatsApp a Zauren Islamic sunnah+2348065575014
Ko adireshin email
(saboawaisu01@gmail.com)

Post a Comment (0)