SHIN DOLENE SAI MIJINA YA AMINCE KAFIN NAYI AMFANI DA MAGANIN TSARIN IYALI..?
19/4/ 2017
TAMBAYA
Assslam alaika Dr inada tambaya inaso nayi amfani da maganin tsarin iyali shin dolene sai mijina ya amince kafin nayi ?
AMSA
To yar uwa dolene sai mijinki ya amince kafin kiyi amfani da wannan magani domin kuwa haka Allah yace mazaje sune suke sama da mata sannan sune suke tsaye akansu saboda abinda Allah ya fifita shashinsu akan shashi (suratul nisa'i ayata 34)
Imamu ibn khasir cikin tafsirinsa yake cewa mijin mace shine shugabanta kuma jagoranta sannan shine mai ladabtar da ita idanta kauce, don haka bazaki iya zuwa aikata abinda ya shafi tsarin iyali bada izinin mijinki ba domin kuwa ya'yan da za'a haifa nasane kuma hakkin sane ya sadu dake dominki samu haihuwa' ba daidai bane aje ayi bada izinin saba. Musamman matan da basusan haihuwa da miji kawai sai suje su yaudaresa suyi tsarin iyali hakika wannan zaluncine kuma ha'inci ne
Amma idan akwai yanayin cutuwa kamar mace tana haihuwar daga wannan sai wannan to idan taga akwai cutuwa akan haihuwar koda bai amince ba zata iya zuwa tayi domin tsare lafiyarta da rayuwarta amma a zauna a fahimci juna tsakanin miji da matar ayi sulhu shine mafi alkairi
Allah shine mafi sani
Amsawa
Dr Abdallah Gadon kaya
Tags:
Tambaya Mabudin Ilimi