Assalamu Alaikum
.
.
Tambaya ta 2,103
.
Wata ce naga zatayi sallar tarawih sai ta kunna karatun Qur'ani tasa earpiece,wai sai ta rinka bin karatun sabida ta tsawaita sallar.shin yin hakan ba laifi?
.
.
.
Amsa
.
..
Qwarai kuwa akwai laifi domin kuwa hakan datayi bidi'a tayi babu wanda yasata yin hakan
Alqur'ani yakamata ta dauka ta riqe tana kallo tana karantawa, inkuma bata iya karatunba, saita samu wata sura wacce ta haddace koda qulhuwallahu ne, sai takama qulhuwallahu tayita maimaitawa taita maimaitawa, kai koda aya daya rak ta haddace to ya halasta kiyita maimaita wannan ayar harki gama tsayuwar kamar Ilahinnas misali wannan ayar ace ita kawai ka iya acikin alqur'ani toh babu laifi kayita maimaitata har kagama tsayuwan darenda zakayi, domin hadisi ya tabbata manzon Allah (s.a.w) yayi tsayuwar dare guda babu ayarda yake karantawa face wani yankin wata aya can qarshen suratul ma'ida, Intu'azzibhum... Wannan yankin ayar itace yayita maimaitawa har yagama tsayuwar dare, kuma kasan dai tsayuwar Annabi ba irin taka bace
…
…
.
Allah yasa mudace
.
.
.
DAGA ZAUREN
.
SHEIKH JAFAR MAHMYD ADAM
.
Watsaps
08161884309
.
.
ﺳﺒﺤﺎﻧﻚ ﺍﻟﻠﻬﻢ ﻭﺑﺤﻤﺪﻙ, ﺃﺷﻬﺪ ﺃﻥ ﻻ ﺇﻟﻪ ﺇﻻ ﺃﻧﺖ، ﺃﺳﺘﻐﻔﺮﻙ ﻭﺃﺗﻮﺏ ﺇﻟﻴﻚ.
.
Subhanak Allahumma wabi hamdika ash hadu anla ila ha illah anta astagfiruka Wa,atubu ilaika