JINI YA DAUKE MATA KAFIN ASHA RUWA

Assalamu Alaikum
.
.
Tambaya ta 2,106
.
Menene hukuncin matar da jini ya dauke mata kafin asha ruwa zata kame Baki ne   na sauran wunin ranar??
.
.
.
Amsa
.
..
Zahirin gaskiya babu wani abu waishi kamun baki acikin Sunnar Annabi muhammad (s.a.w) kawai Ijtihadine na wayansu malamai suke cewa wai ayi kamun baki, amma wannan maganar batada wani wajahi ko dalili daga Alqur'ani ko Sunnar Annabi muhammad, kawai qoqarinsu ne su wayancan manyan malamai, amma abinda yafi dacewa shine abar musu ijtihadinsu sai ayi musu addu'a amma baza,ayi aiki dashiba

         Dan haka wannan zata cigaba da cin abincinta babu wani kama bakinda zatayi, kawai abinda yatabbata a sunnah shine in kana azumi to azumin kakeyi, in kuma baka azumi to bakayi kawai kaci abincinka, amma babu wani zancen kamun baki

     Zamuyi qarin bayani akan wannan kamun bakin nan gaba kadan insha Allahu


.
Allah yasa mudace
.
.
.
DAGA ZAUREN
.
SHEIKH JAFAR MAHMUD ADAM
.

Watsaps
08161884309

.
.

.
ﺳﺒﺤﺎﻧﻚ ﺍﻟﻠﻬﻢ ﻭﺑﺤﻤﺪﻙ, ﺃﺷﻬﺪ ﺃﻥ ﻻ ﺇﻟﻪ ﺇﻻ ﺃﻧﺖ، ﺃﺳﺘﻐﻔﺮﻙ ﻭﺃﺗﻮﺏ ﺇﻟﻴﻚ.
.
Subhanak Allahumma wabi hamdika ash hadu anla ila ha illah anta astagfiruka  Wa,atubu ilaika

Post a Comment (0)