CIKAKKEN BAYANI GAMEDA ZIKIRI BAYAN KIRAN SALLA

CIKAKKEN BAYANI GAMEDA ZIKIRI BAYAN KIRAN SALLA

      TAMBAYA

Assalam malam Dan inason amini cikeken bayanin abin da mutun Zeke fada a yayin kiran sallah da kuma bayan Angama
Ma'ana addua'o in

      AMSA

Wa alaikumus salamu warahmatullah.

❗1). A. Annabi Sallallahu alaihi wasallam yace :( IDAN KUKAJI KIRAN SALLAH, TO KUFADI DAI DAI DA ABINDA MAI KIRAN SALLAR YAKE FADA).
👉🏿 Buhari: 611.
👉🏿 Muslim:383.
Daga Abu Sa'id Alkhuduriy Allah yakara masa yarda.
❗  B. A Hadisin Umar Allah yakara masa yarda. Annabi Sallallahu alaihi wasallam yace: ( IDAN LADAN YACE: ALLAHU AKBARUL LAHU AKBAR, SAI DAYANKU YACE: ALLAHU AKBARUL LAHU AKBAR, SANNAN YACE:: ASH HADU ALLA ILAHA ILLLAH, SHIMA YACE: ASH HADU ALLA ILAHA ILLALLAH, SANNAN YACE: ASH HADU ANNA MUHAMMADAR RASUULULLAH, SAI SHIMA YACE:  ASH HADU ANNA MUHAMMADAR RASUULULLAH, SANNAN YACE: HAYYA ALAS SALAH, SAI YACE: LA HAULA WALA KUWWATA ILLA BILLAH, SANNAN YACE: HAYYA ALAL FALAH, SAI YACE: LA HAULA WALA KUWWATA ILLA BILLAH, SANNAN YACE: ALLAHU AKBARUL LAHU AKBAR, SAI SHIMA YACE: ALLAHU AKBARUL LAHU AKBARULLAHU AKBAR, SANNAN YACE: LA ILA ILLALLAH, SHIMA YACE: LA ILAHA ILLALLAH DAG ZUCIYARSA, TO YA SHIGA ALJANNAH).
👉🏿 Muslim: 385.
👉🏿Abu dawud: 523.
❗2). A. Bayan kiran sallar sai ayi wadannan addu'o'in:
Allahumma salli ala Muhammadin wa ala ali Muhammadin kama sallaita ala Ibrahima wa ala ali Ibrahima innaka hamidun majid. Allahumma barik ala muhammadin wa ali muhammadin kama barakta ala Ibrahima wa ala ali Ibrahima Innak hamidun majid
Inkayi wannan Annabi yace: ( Allah zaiyi maka goma.
👉🏿Muslim: 384.📒
👉🏿 Abudawud: 523.📕
👉🏿 Tirmiziy: 3695.📗
Dan Amru Allah yakara masa yarda.
⚡B. Wa ana ash hadu alla ilaha illallah, wahdahu la sharika lah, wa ash hadu anna Muhammadan abdahu warasulah, raditu billahi rabban wabil islami dinan, wabi Muhammadin rasulan. Annabi yace:( DUK WANDA YAFADI HAKA BAYAN YAJI KIRAN SALLAH, ANGAFARTA MASA ABINDA YAGABATA NA DAGA ZUNUBBANSA).
👉🏿 Muslim: 386. 📒
👉🏿Abu dawud: 525.📕
👉🏿 Tirmiziy:21📗.
Daga Sa'ad Bunu Abi Wakkas Allah yakara masa yarda
❗C. Allahumma rabba hazihid da'awatit tammah, wassalatil ka'imah ati Muhammadanil wasilata walfadilah, wab as'hu maka'man mahmudanil lazi wa adtah.
Annabi yace: ( DUK WANDA YAFADI HAKAN BAYAN KIRAN SALLAH, CETONA YA HALATTA AGARESHI RANAR KIYOMA).
👉🏿Buhari: 614📚.
👉🏿Abu dawud:529.📙
👉🏿 Tirmiziy: 211📒.
Daga Jabir Allah yakara masa yarda.
❗D. Sai kayi addu'ar bukatarka ta duniya da lahira
Annabi Sallallahu alaihi wasallam_ yace: (ADDU'A TSAKANIN KIRAN SALLAH DA IKAMA, KARKABBACE).
👉🏿 Abu dawud: 521.📕
👉🏿 Tirmiziy: 212📗.
👉🏿 Ibnu khuzaimah: 425📚.
Daga Anas Allah takara masa yarda.

Karin bayani:
✔1. Wajen hayya alassalah da falah( حي على الصلاة/ حي على الفلاح
, La haula zakace,  sau duka hudun.
✔2. Karshen Ash hadu alla ilaha illallah, ba acewa wahdahu la sharika kalah, sai ankamma kiran sallar za'ayi, munkawo addu'ar.
✔3. Za'abi ladan kalma kalma.
✔4. Ko sau nawa kaji kiran sallar zakayi mai mai abinda yake fada, koda masallatai nawane.
✔5. Ikama ma zaka maimaitata kamar yadda yake akiran sallah. Amagana mafi inganci.
✔6. Idan ladan yace: Ash hadu, sai kace: wa ana, ya wadatar.
👉🏿Buhari: 914. 📙
✔7. Ba'ayin addu'a bayan tada Iqamah.

👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇
والله تعالى أعلم
〰〰〰〰〰〰〰〰〰〰〰
✏ _AMSAWA_:🖊
SHAFI'U SHEHU MINNA
(☎ *08033410797) 
daga zauren:
ISLAMIC GROUP 1 & 2_🌙
👆🏼👆🏼👆🏼👆🏼👆🏼👆🏼👆🏼👆🏼👆🏼👆🏼👆🏼

Post a Comment (0)