ZAN IYA SADUWA DA MAI HAILA, IDAN NA SA CONDOM?

ZAN IYA  SADUWA DA MAI HAILA, IDAN NA SANYA CONDOM ?
    

Tambaya

Assalamu Alaikum. Malam Allah ya karama daukaka da imani. Ga tambayata: Shin mutum zai iya saduwa da matarsa idan tana Haila matukar yasa Condom?

                           
Amsa
Wa'alaikum assalam.

To dan'uwa bai halatta ka sadu da mai haila ba ko da kuwa ka sanya Condum, saboda Allah ya haramta saduwa da mai haila, kuma ya kira jinin haila a aya ta 222 a suratul. Bakara da cuta, sannan ya rataya halaccin saduwa da mace mai haila da abubuwa biyu wato: yankewar jini da kuma yın wanka.                                                      
Ba namiji ne kadai haila take iya cutarwa ba, idan ana saduwa da mace mai haila mahaifarta za ta takure sai jini ya barke mata, wannan sai yake nuna cewa: ba za'a sadu da mace mai haila ba ko da an sa Condum .
          
Allah ne mafi sani.

Dr. Jamilu Zarewa
 
28/11/2015

Ga dukkan mai son shiga ZAUREN FIQHUS SUNNAH Sai ya yi saving wannan number+2348122348585 sannan ya tura da sunnasa da adireshinsa ta what'sApp. Duk abun da mutum ya turo matukar ba suna ba ne ba za a kula shi ba.

Post a Comment (0)