MAGANGANUN MALAMAI GAMEDA HUKUNCIN TURA SAKONNIN HAPPY JUMU'AT

MAGANGANUN MALAMAI GAME DA HUKUNCIN TURA SAKONNIN

HAPPY JUMU'A;

JUMU'A MUBARAK;

JUMU'AH KAREEM;
da sauransu

A haqiqanin gaskiya wannan bashi da asali daga Magabata, kamar yadda manyan malamai suka bada fatawowi akai kamar haka:

-An tambayi Sheikh Fauzan Fauzan:

Menene hukuncin Musulmi yacema dan'uwansa Musulmi Jumu'a Mubarak a kowacce Jumu'a, ta hanyar turawa a waya da sauransu?

Sai yace:

"هذا لا أصل له، وهو بدعة، ولا يجوز التهنئة بيوم الجمعة، هذا لم يرد فيه شيئ، وليس من عمل السلف، فهو مبتدَع، والمبتدعة يستغلون الآن الجوالات والإنترنتات -على ما يذكرون-؛ ويستعملونها لترويج البدع؛ بهذه الطريقة."

Ma'ana:
Wannan baida asali kuma yin hakan bidi'ah ne, ba'a yadda mutum yarinka taya mutane murna ba, domin ba'a samo wani nassi akan haka ba, kuma bashi daga cikin aikin magabata wato. Wannan fararren abune, sannan kuma yan bidi'a suna yada wannan acikin wayoyi da internet, kuma suna anfani dashi domin yada bidi'a ta wannan hanyar.

-Shi kuma,  Sheikh Ahmad bin Yahya Annajmi (Rahimahullah) cewa yayi Kamar haka:

Yawaita kalmar JUMU'AH MUBARAK Shin haka ya hallata?

Sai yace:

"لم نعرف هذا عن السَّلف."

Ma'ana:
Bamusan wannan daga magabata ba.

-Haka kuma an tambayi Sheikh Abdulmuhsin Al-Abbad Kamar haka:

السؤال: -بناء على أن يوم الجمعة يوم عيد- هل يجوز التهنئة فيه كأن يقال: "جمعة مباركة" أو "جمعة متقبلة"؟

Ma'ana:
Idan muka dauki Jumu'a ranar idice,  shin ya hallata murinka taya juna murna aranar, Kamar mutum yace JUMA'A MUBARAK, ko kuma JUMA'A MUQABBALAH?.

Sai yace:

والله- ما نعلم شيئا يدل على هذا، أما بالنسبة لعيد الفطر، والعيدين فقد جاء عن الصحابة أنه كان إذا لقي بعضهم بعضا قال: "تقبل الله منا ومنكم" أو "تقبل الله طاعتكم").

Ma'ana:
Wallahi bamusan wani abu dake nuni akan hakan ba,
Amma Kamar idil fitr da kuma iduna guda biyu, haqiqa yazo daga sahabbai cewa idan dayansu yahadu da daya yana cemasa ALLAH YA KARBA MANA KUMA YA KARBA MUKU, Kokuma ALLAH YA KARBI BIYAYYARKU.

-Haka an tambayi Sheikh Abdul'aziz bin Abdullah Âl Sheikh cewa: Menene hukuncin fadin JUMA'A MUBARAK?

Sai yace:

ما لها أصل، يبثون في الجوال يوم الجمعة: "جمعة مباركة"، هي الجمعة مباركة بلا شك، وأن الله تعالى خصنا به، وقد أضل عنه اليهود والنصارى، لكن التهنئة به كل جمعة ما أعلم له أصلا.

Baida asali, suna turawa awaya ranar Jumu'a, JUMA'A MUBARAK
Ko shakka babu cewa ita ranar mai albarkace kuma Allah ya kebance mana ita, kuma an batar da Nasara da Yahudu daga gareta, to saidai taya murna acikinta bansan yanada asaliba.

-An tambayi sheikh bin Baaz Allah yajikansa: yayi dogon bayani dakuma tsoratarwa akan bid'a, akarshe dai yake cewa:

Idan mutum yana cewa dan uwansa wani lokacin batare da ya dawwama akantaba kuma bai yarda da cewa an samota anassi ba, kawai dai ta hanyar addu'a, to ina kwadayin hakan bazai zamo laifi ba. 

Amma barinta yafi domin kar ta zama Kamar sunnar data tabbata.

Yan'uwa! Wajibine mu nisanci bid'a ko yaya take.

Domin Manzon Allah ya tsoratar damu akan bid'a, kamar yadda yazo acikin hadisai da dama, daga ciki akwai irin hadisin da Bukhari ya fitar kamar haka:

عن النبي -صلى الله عليه وسلم- أنه قال: من عمل عملا ليس عليه أمرنا فهو رد. رواه مسلم والبخاري معلقا، وفي لفظ لهما:
من أحدث في أمرنا هذا ما ليس منه فهو رد.

Don Allah muji tsoron Allah mu kiyaye.

Allah yasa mudace.

Sabon tsari

*Ahmad El-Maude Zaria*

Daga kafarku mai Albarka
👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻
Daarus-sahaabah Network Zaria, kaduna state, Nigeria.
+2347036108733

Post a Comment (0)