MIJINA BAYA BIYAMIN BUKATA, MENENE SHAWARA

MIJINA BA YA BIYA MIN BUKATA, MENENE SHAWARA ?

Tambaya

Assalamun alaikum, Malam mace ce mijinta ba ya iya biya mata bukata saboda raunin mazakutarsa, kuma ashe abin da ya raba shi da uwar gidansa kenan.

Kasancewar ba ya biya mata bukata ta shiga cikin halin damuwa, sannan ta yanke shawarar cewa: in ya kira ta shimfidarsa ta daina zuwa, to malam ta yi laifi game da wannan shawarar da ta yanke ?

Amsa
Wa alaikum assalam,

A shawarata  kamata yayi a kira magabatansu su xauna su tattauna a gano yadda xa'a warware matsalar.

Idan har ya tabbata ba cikakken namiji ba ne to xa'a bashi shekara daya ya nemo magani.

Idan ya warke shikenan, in bai warke ba kuma xa ta iya fadawa cikin haram idan taci gaba da xama dashi, to ya halarta a raba auran, kamar yadda aka raba da uwar gidan.

Yana daga cikin manyan manufofin aure: ma'aurata guda biyu su katange junansu daga haram, in har aka rasa wannan to akwai matsala a xamantakewar aure.

Allah ne mafi sani.

*Dr, Jamilu Zarewa*

22/11/2017

Ga dukkan mai son shiga *ZAUREN FIQHUS SUNNAH* sai ya yi saving wannan number +2348122248585  sannan ya tura da sunansa da adireshinsa ta whatApp. Duk abun da mutum ya turo matukar ba suna ba ne ba za a kula shi ba.

Post a Comment (0)