MASU HIKIMA SUN CE

*```🇲A$U HIKIMA SUNCE:‼*```

_Kada ka dauka cewa, duk wanda ya yi shiru kurma ne. Wani ya yi shiru ne yana jiran lokaci. Wani ya yi shiru ne dan yana nazari. Wani kuma kawaicinsa shi ne maganarsa._

_Kada ka damu idan kana yi ba a godewa. Magabata sun ce, aikin jama'a ba a iyawa, ba a gamawa, ba a yabawa. Idan Allah ya yaba aikinka ya ishe ka._

_Yawan jayayya alamar girman kai ne. Yawan surutu alamar tabuwar hankali ne. Kawaici ado ne. Kyauta halin girma ne. Yafiya daukaka ce. Yabon Kai kuwa shi ne tsabar jahilci._

_Zamani ya canza : A da idan ka zagi wani kowa Sai ya kau da kansa. A yau idan za ka ci naman dan uwanka Har ruwan wanke baki ake ba ka._

_Idan kana cikin damuwa ka jira samun sauki daga wurin Allah, wannan jiran da kake yi ibada ne. Domin kyautata zato ne ga Allah. Wanda ya kyautata ma Allah zato kuwa lallai ne Allah zai ishe shi._

_Mutum kamar fensir ne. Rayuwa za ta rika feke shi yana sake rubutu har ya zo ya kare. Idan ka mutu babu abinda zai rage sai abinda rayuwarka ta rubuta._

_Kowane ma'aikaci yakan zauna a gaban tebur masu bukata suna tsaye a gabansa. Amma ban da malamin makaranta. Shi kam a tsaye yake dalibansa na zazzaune kamar sarakai a kan kujeru. Girmama malaminka girmama Allah ne._

_Mafi hankalin mutane shi ne wanda ya bar duniya tun kafin ta bar shi, ya gyara kabarinsa tun kafin ya shiga cikinsa, ya yardar da ubangijinsa tun kafin ya hadu da shi, yayi sallah a cikin jama'a tun kafin su sallace shi, sannan ya yi wa kansa hisabi tun kafin ayi masa. Yau ranar aiki ce, ba hisabi, gobe ranar hisabi ce ba aiki._

_Idan yaro ya yi kwana bakwai za ayi masa suna. Idan ya shekara bakwai zai fitar da hakora. Idan ya kara bakwai sai ya yi mafarki. Bayan wasu bakwai ya kammala tsawonsa. Idan ya kara bakwai ya kammala hankalinsa. Daga nan kuma yau da gobe ita ke koya masa rayuwa._

_Dan Adam na da ban mamaki. Wani bai iya karanta ko aya goma na Alkurani a kowace rana, amma yana karanta sako dari a wayar tafi-da-gidanka. Idan ka tambaye shi zai ce bai da lokaci. Lahira akwai hisabi! Akwai kallo!!_

_Za ka iya rayuwa a cikin bene kana kuntata. Wani kuma yana a cikin bukka yana jin dadi. Rayuwa mai dadi a zuciya take ba a kyawon gida ko dadin abinci ko walkiyar tufafi ba._

_Ba za ka iya ganin fuskarka a cikin ruwa ba idan yana tafasa. Kamar haka ne ba za ka iya ganin gaskiyar lamura ba idan kana cikin fushi. Kama bakinka idan zuciyarka na tafasa. Magana a cikin fushi ba ta haifar da alheri._

_Mutum yakan shiga wani yanayi Sai ya dauka cewa karshensa ya zo kenan. Amma daga bisani Sai ya gane cewa, wannan shi ne farkon Jin dadin sa a duniya. Da yawa kofar da kake zaton ta a kulle Idan ka tura ta za ka same ta a bude tana jiran isowar ka. Kada ka yanke kauna daga alheri. In da rai Abin mamaki : A kyauta ake shiga Masallaci amma ka gan shi ba kowa. Wuraren shashanci biya ake yi amma ka gan su makil da jama'a. Mutane suna barin garabasar Aljanna, suna sayen wuta da kudadensu._

_Idan ka shiga gidan mutane ka mayar da kanka makaho. Idan ka fito ka koma kurma. Kamar yadda ba ka son a leki asirinka kuma a yada shi, haka su ma mutane ba su son a leki nasu ko a yada shi._

*〰〰〰〰〰〰〰〰〰〰*
*```DAGA:*```    
       *```ZAUREN:*```
*```©📚DAARUL ILMI:📚✍🏼*```

📔📓
```Wђaт$aρρ```
+2348146556423

*〰〰〰〰〰〰〰〰〰〰*
*🇿akυ Iya $amυπ $ђaŦiπmυ A Ŧaςєвooк Taπaπ👇🏼👇🏼👇🏼*

https://mobile.facebook.com/Daarul-ILMI-1395795197196573/

4 Comments

Post a Comment