DA KE NAN HAKA ZA SU CE

DA KE NAN HAKA ZA SU CE




Yayin da mijinsu ba shi da shi, ita Kuma tana aiki tana samu tan da shi.

"To ai kai Allah Ya dora wa ka nemo, -naka na mu ne, na wa kuwa na wa ne".

Nana Khadija ke nan da ta yi gori, ta ki ba da nata, ta ce je ka nemi naka. Hasha ha!

Da ke nan da Manzon Allah (SAW) yake shigowa gida ya ce: "Kuna da wani abu ne (da zan samu) na ci?". 

Da sai su yi caraf su ce: Ka kawo ne ballantana ka sa rai.

Wannan ba a gidan Manzon Allah (SAW) kadai yake faruwa ba, sahabbai na zuwa su tambayi matayensu, ko suna da abinci (wanda shi bai samu ba, bai kawo ba) ko ya samu ya ci.

 Karanta sababin saukar ayar halatta kusantar iyali da dare da azumi a Bukhari.

Yanda yake fa a Musulunci; namiji zai ciyar da iyalinsa, Idan ba shi da shi to ita Kuma Idan ta dauki nauyi, to shi ne Manzon Allah (SAW) ya ce mata ta yi: بر وصلة

"Ta Yi biyayya ga Allah ta nagarta, Kuma ta Kara dankon zumunci".

Fahimtar addini daban, kuma riko da Feminisanci daban. Mutum Yana da damar daukan wanda yake so, 'yancin mutum ne ya bi Macron. Illa iyaka.

# Dr Abdulkadir Isma'il 

https://t.me/miftahul_ilmi
Post a Comment (0)