Asssalamu Alaikum
.
.
Tambaya ta 2,782
=
Naje wani masallaci sallar asubahi bayan liman yagama karanta fatiha da surar karshe sai yayi ruku,i bayan yadago daga ruku,i sai Naga yadaga hannuwa sama yana addu,a sukuma mamu sunacewa Amin shin wannan abun yatabbata a sunnah
=
=
Amsa
=
=
Toh A zahirin gaskiya wannan be tabbata a sunnar Annabi Muhammad (s.a.a) ba, kuma be tabbata ba daga cikin Aikin Sahabban Annabi (s.a.w) musamman Khulafa'ur Rashidin duk wannan ba sunnarsu bace, asalin sunan yanka na wannan aikin shine bidi'a ne kawai kamar yadda hadisi ya tabbatarda hakan acikin Bulughul marami zaka iya samun hadisin cewa wannan aikin bidi'a ne.
Amma tayiwu qila su wadannan daka samu sunayin wannan a sallarsu ba 'yan bidi'a bane qila Qarancin ilimine yake tare dasu basu san karatunba kokuma qila irin masu maqalqalewa mazhaba dinnan ne kasamu musammab dayake a mazhabar Malikiyya yin qunuti tutur a sallar asubahi kafin ruku'i kokuma bayan ruku'i, kai su a malikiyya ma kwata kwata basayin quniti inbanda sallar asubahi basayin qunutin wutri kuma basayin qunuti idan wani bala'i ya samu musulmi, shiyasa yana daga cikin abin mamaki aqasarnan zakaji mutum yana cewa kar abi kowa inbanda Malikiyya sekuma kaganshi yana yin qunuti idan ana rikicin siyasa ko ta Addini, amma malikawa ko za'a kashe duk musulman duniya to babu yin qunuti a mazhabarsu sedai wannan na asubahin sekuma a witrin kwanaki goman qarshen watan ramadan ananne kawai malikiyya ta yarda ayi qunuti, wannan bayanin yananan acikin mudauwanah.
Mazhabar shafi'iyya suma suma sunayin qunuti bayan dagowa ruku'in sallar asubahi kullun tutur, ammafa duka wannan ba sunnah bace kamar yadda mukayi bayani, amma daga hannaye alokacin da liman yakeyin qunuti da fadin Ameen wannan duk sun tabbata daga magabata, amma banda shafawa a Fiska.
A taqaice dai wannan aikinda kaga anayi a wannan masallaci babu shakka shi aikinda sukeyi bidi'ane amma be zama lallai ace suma sun zama 'yan bidi'aba ta iya yiwuwa qila sunada wani uziri ko tawili
=
=
Allah yasa mudace
.
.
DAGA ZAUREN
.
KITABU WAS SUNNAH
.
مجلس تعليم الكتاب والسنة
📓📔
Watsaps
08036222795
08136182627
.
.
Zaku iya samun shafinmu na facebook ta wannan hanyar
http://m.facebook.com/Kitabu-Wassunah-1522000298067561/
.
ﺳﺒﺤﺎﻧﻚ ﺍﻟﻠﻬﻢ ﻭﺑﺤﻤﺪﻙ, ﺃﺷﻬﺪ ﺃﻥ ﻻ ﺇﻟﻪ ﺇﻻ ﺃﻧﺖ، ﺃﺳﺘﻐﻔﺮﻙ ﻭﺃﺗﻮﺏ ﺇﻟﻴﻚ.
.
Subhanak Allahumma wabi hamdika ash hadu anla ila ha illah anta astagfiruka Wa,atubu ilaika