Asssalamu Alaikum
.
.
Tambaya ta 2,781
=
Inada aboki christa abokinane sosai ana bikin sa kuma ya gayyaceni shin ya halatta inje kuma acikin coci ake daurin auren ta halatta in shiga?
=
=
Amsa
=
=
Aa bai halasta musulmi yashiga coci saboda amsa gayyatar wani arne kamar wannan ba, malamai sunce haramunne musamman dayake akwai fushin Allah wanda yake sauka awannan wajen a kowacce daqiqa, Amma idan ba a coci bane za'a daura auren malamai sunyi sa6ani akai, sedai mafi ingancin magana shine idan ba a coci bane kana iya zuwa matuqar dai baza'a cakuda maza da mata a wajenba kuma baza'a aikata shirka ko wani sa6on Allah a wajenba shine yake halasta kaje, Kaji sharuddanda ake bukata su cika kafin kaje, na farko yazama ba a coci za'ayiba, na biyu babu shirka a wajen, na Uku babu cakuda maza da mata, na Hudu bazasu aikata haramun a wajenba, wanda kuma zeyi wuya ace bikin arne ya wofinta daga wadannan hudun zeyi wahala matuka su iya cika wadannan sharudda, saboda haka mafi zaman lafiya shine rashin zuwan yafi natsuwa ga musulmi
=
=
Allah yasa mudace
.
.
DAGA ZAUREN
.
KITABU WAS SUNNAH
.
مجلس تعليم الكتاب والسنة
📓📔
Watsaps
08036222795
08136182627
.
.
Zaku iya samun shafinmu na facebook ta wannan hanyar
http://m.facebook.com/Kitabu-Wassunah-1522000298067561/
.
ﺳﺒﺤﺎﻧﻚ ﺍﻟﻠﻬﻢ ﻭﺑﺤﻤﺪﻙ, ﺃﺷﻬﺪ ﺃﻥ ﻻ ﺇﻟﻪ ﺇﻻ ﺃﻧﺖ، ﺃﺳﺘﻐﻔﺮﻙ ﻭﺃﺗﻮﺏ ﺇﻟﻴﻚ.
.
Subhanak Allahumma wabi hamdika ash hadu anla ila ha illah anta astagfiruka Wa,atubu ilaika
Tags:
Tambaya Mabudin Ilimi